Dalilan korar daliban Jami’ar Bayero 63

0

Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK), ta bayyana dadilan cewa shiga harkallar satar jarabawa daban-daban ya haifar da kokar dalibai har 63 da hukumomin makarantar suka yi.

Daraktar Shirya Jarabawa, Daukar Dalibai da Taskace Bayanai (DEAR), Amina Umar Abdullahi ce ta sanar da haka, tare da Karin bayanin cewa an kuma yi wa wasu dalibai dafkal har ya tsawon shekara daya.

Ta ce wannan tsatstsauran hukunci ya biyo bayan shawarwarin da Kwamitin Hukumar Gudanarwar Jami’ar ya kafa a kan satar jarabawa, kuma ya gabatar da bayanin sa a ranar Laraba, 28 Ga Agusta, 2010.

An dai kama daliban daga Tsanyayoyin Jami’ar daban-daban. Kuma akwai wasu 19 da aka rubuta wa takardar gargadi da jan-kunnen shiga taitayi.

Satar jarabawa ta zama ruwan-dare a manya da kananan makarantun kasar nan. A gefe daya kuma ana fama da matsalar zargin lalata da malaman Jami’ar ke yi da wasu dalibai mata, su na ba su makin cin jarabawa a matsayin lada.

Ana kuma fama da masu yi wa dalibai mata barazanar idan ba su bayar da kan su an yi lalata da su ba, to ba za ci jarabawar malamin ba.

Share.

game da Author