Sojoji sun kama Chukwudi da ke saida wa Boko Haram ‘kayan aiki’ a hanyar Baga

0

A ranar Lahadi ne aka bayyana kama wani da ake zargin cewa ya na saida wa Boko Haram da kayayyakin masarufi a Jihar Barno.

Kwamandan Rundunar GOC ta 7, AK Ibrahim ne ya gabatar da shi ga manema labarai a Sansanin Gubio na Musamman da ke Maiduguri.

An kama wanda ake zargin da tsoffin tayoyin babura har guda 136 da kuma sabbin tib na tayoyin babura 200. Sai kuma gam na facin taya.

Ibrahim ya ce an kama Samuel Chukwudon a kan hanyar Baga zuwa Munguno. Kuma an kama har da motar da ya ke tafe da ita.

Ya ce sun tabbatar hanyar Tafkin Chadi ya dosa, inda Boko Haram suka yi kaka-gida, su na amfani da Babura su kai hare-hare.

Ya kara da cewa dalili kenan ma sojoji suka hana amfani da babura ko saida kayan babura.

Sai dai kuma labari ya sha bamban a lokacin da ‘yan jarida suka tambayi Chukudon. Cewa ya yi shi ba Boko Haram ya ke saida wa kaya ba.

“Ni a Monguno na ke da zama tun 1990. Kuma a hanyar tafiya ta zuwa Monguno su ka kama ni. Ina saida wa masu kurar saida ruwa tsoffin tayoyin babura ne, a Monguno su na daura wa kurar daukar ruwan su.

Kwamandan sojoji dai ya ce Chukwudon ya yi kokarin bada kudi a kyale shi a lokacin da aka kama shi. Kuma a lokacin da ake binciken sa ma ya yi kokarin bada kudi domin a kyale shi.

Daga nan ya sanar da cewa za su kona dukkan abin da suka kama a hannun Chukwudon.

Share.

game da Author