MIYETTI ALLAH: Za mu iya wadata Najeriya da madara ba sai an rika shigowa da shi ba

0

Sakataren Kungiyar Fulani Makiyaya na Miyetti Allah Othman Ngelzarma, ya bayyana cewa yawan makiyayan dake kasa Najeriya sun isa ace kasar na cike da wadatar madara ba sai an rika shigowa da shi daga kasashen waje ba.

Ngelzarma ya bayyana haka ne da yake tattaunawa da wakilan Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja ranar Talata.

” A yanzu haka ina so in tabbatar muku da cewa akwai akalla shanu miliyan 70 da ake kiwo a fadin kasa Najeriya, sai dai kash, babban matsalar da ake samu shine babu kamfanonin sarrafa madaran shanun koda an fiddo shi daga rugage.

” Babu wuraren da fulani za su rika kai nono a na siya domin sarrafa shi. Karshen ta sukan kare ne saidai su fita da shi talla a kwarerayi suna siyarwa da arhan gaske sannan kuma ana asarar da yawa.

” Da ace za a samar da wuraren siyar da nonon shanu idan aka tatso sannan kuma ace akwai kamfanonin da ke sarrafa shi ya zama madara da hakan zai wadata kasar da madara ba sai an rika shigowa da shi daga kasashen waje ba.

” Yanzu bari in baku labarin wani kamfani da ake kira ‘L and Z youghurt da ke Kano’. Shi kam babu ruwan sa da wahalar madara domin a kamfanin sa duk makiyaya dake wannan kewayen basu tallan nono. Da zaran an tashi da safe sai kawai mutum ya garzaya da nonon sa ‘L and Z’ su auna sannan su biya. Wasu da dama ma basu yawace yawacen kiwo domin burin su samar wa kamfanin da nono a kullum su cake kudaden su a aljihu.

” Gaba daya fulani makiyaya da ke zagayen wannan kamfani a Kano sun saka ‘ya’yan su a makarantun Boko suna karatun su. Sannan kuma domin tallafawa iyayen yaran dake makaranta, kamfanin ta kara naira 20 a kowani litan nono, domin goya wa iyayen baya su iya biyan kudin makarantan ‘ya’yan su.

A karshe Ngelzarma ya yi kira ga gwamnatin tarayya da na jihohi da su kakkafa kamfanoni domin makiyaya su rika siyar da nono domin ci gaba da bunkasa tattalin arzikin kasa.

Share.

game da Author