RAYUWAR MATAN SULEJA: Masu wahalar sana’ar fasa dutse babu ribar kirki

0

Da wahalar gaske ka samu aikin karfi wanda ya yi fasa dutse wahala. Noma bai kai shi wahala ba. Haka daka ko sussuka da jima ba su kai fasa dutse wahala ba. Sana’ar da kawai za a iya cewa ta sha gaban fasa dutse wajen wahala, watakila sai dai ko kira da sassaka.

Sai dai wannan wahala da ake sha a sana’ar fasa dutse, bai hana mata manya da kanana shiga cikin sana’ar ba.

A irin wannan hali wakilin mu ya samu wata karamar yarinya mai shekaru 12 mai suna Racheal, ta na rike da makwalkwasar bugun dutse, ta na duka ta na maida shi kananan duwatsu ko buraguzai.

Racheal ta bayyana wa wakilin mu cewa a rana ta na fasa dutse ta mayar da shi kananan duwatsu ko tsakuwa da ka iya cika buhun siminti hudu. Masu aikin gini ake saida wa duwatsun.

Da wannan ‘yan kudi da Racheal ke samu ta ke taimakawa wajen ciyar da mahaifiyar ta da sauran biyan bukatun iyalin su gaba daya.

“Da kudin da na ke dan tarawa na ke sayen tufafi da takalma, sauran kudi kuma na kan kai wa mahaifiya ta domin ta rika sai mana abinci.” Inji Racheal.

Idan wani ya ga irin yadda Racheal ke takarkarewa ta na fasa dutse, zai yi tsammanin wata baligar yarinya ce. Amma karamar yarinya ce ‘yar karamin ajin sakandare, wato JSS2.

Da aka tambaye ta dalilin da ya sa ya ke aikin fasa dutse a lokacin da ake karatu, sai Racheal ta ce an kore ta ne daga makaranta saboda kasa biyan kudin makaranta.

“Naira 6,000 ne kudin makarantar. Mun cirza mun kai musu naira 3,000, amma sai makaranta ta ce kudin bai cika ba. Don haka ba a son gani na a cikin makarantar.”

Aikin fasa dutse da hannu sana’a ce a ciki da kewayen wajen Suleja, saboda karancin injinan fasa dutse a yankin.

Za a rika ganin su a gefen titi, inda suke amfani da ‘hama’ ko makwalkwada su na fasa dutse domin masu aikin gine-gine su rika saye.

Duk kuwa da cewa a cikin rana mai tsanani suke aikin, ribar da mata da ‘yan matan yankin Suleja masu fasa dutse da hannu ke samu, ba ta taka kara ta karya ba. Ballantana ma a ce ta kai gumin da su ke yi ko kuma wahalar da suke sha.

Salome Linus na daya daga cikin matan da ke kuma sammakon fita aikin sana’ar fasa dutse. Duk da akwai hatsarin gaske na yiwuwar ruftowar wargajejen dutsin da ake bantalowa daga jikin tsauni, Salome ba ta damu ba hakan ba.

“Ina samun gwargwadon buhun sumintin da na cika da duwatsu. Idan na cika buhun siminti daya zan samu naira 200.

Salome ta ce daga Jihar Benuwai ta zo Suleja sana’ar fasa dutse. A rana daya ta kan fasa dutse ta cika buhun siminti biyu zuwa takwas. Kenan ta kan samu naira 400 zuwa naira 1,600 a rana daya.

“Shin idan ban saida buraguzan duwatsu ba, da me zan ciyar da kaina har na ciyar da kananan yaran da na ke da su? Ta yaya zan iya biya musu kudin makaranta kuma?

Salome ba budurwa ko matashiyar mace ba ce. Shekarun ta sun ja, domin cewa ta yi ta kai shekara 52. Kuma da ganin jikin ta ka san ba ta rage ko da shekara daya ba.

PREMIUM TIMES ta gano cewa idan wadannan mata sun fasa dutsen, sukan sayar wa masu aikin gini ne.

Babu ruwan ta da tsananin wahalar da ake sha wajen amfani da karfi ana fasa dutse, natsawar za ta iya samun kudin da za ta ciyar da yaran ta da kuma wasu yara biyar na kanin ta da ya mutu, ya bar mata kula da su.

“Ni ba sabon-shigar sana’ar fasa dutse ba ce. Shekara ta 16 ina wannan sana’a. Farkon lokacin da muka fara, mukan shiga cikin daji mu sungumo ko mu mirgino marga-margan dutse, mu zo bakin titi, mu farfasa shi sannan mu sayar.

“Ana cikin haka ne wata rana miji na ya tafi wurin aiki sai ’yan fashi da makami suka kashe shi. To da wannan sana’a na ke ciyar da yaro na da kuma ‘ya’yan kani na su biyar da mutu ya bar min ina kula da su. Biyar na dauka daga cikin yaran na sa, amma su tara ya mutu ya bari.” Inji Salome.

Amma yanzu ta daina shiga daji ta na mirgino dutse ta fasa, sai dai ta rika saye daga wajen masu mota tifa da ke bi su na sayar musu, su kuma su farfasa su sayar.

“Wani lokaci ma bashi ake ba mu duwatsun, sai mun fasa mun sayar sannan mu biya su. Mu kuma ‘yar ribar da ke sama ita za mu rike mu tafi gida da ita.

“Idan mu ka sayi duwatsun naira 13,000, za mu farfasa mu rika saida kowane buhun simintin da muka cika da dutse naira 200. To na kan samu naira 2,000 riba.

Salome ta ce ba ta taba jiye kudi a banki ba. Cikin ta da cikin yaran da ta ke kula da su, shi ne bankin ta.

Dama Hausawa sun ce sana’ar wani, wani sai dai kallo.

Share.

game da Author