Yunwa na sa a yanke hukuncin da za a yi da na sani daga baya – Binciken Likita

0

Babban likita a jami’ar Dundee, dake Birtaniya mai suna Benjamin Vincent ya gargadi mutane da su rika gujewa yanke hukunci ko kuma daukan matsaya akan wani muhimmin abu idan suna jin yunwa, wato basu ci abinci ba.

Sakamakon binciken da Likita Vincent yayi, ya nuna cewa lallai akwai matukar matsala idan aka yanke hukunci ko aka dauki wani matsaya akan wani muhimmin abu a lokacin da ake jin yunwa yana mai cewa a wannan lokaci kwakwalwar mutum kan dode, bai aiki kamar yadda ya kamata. A dalilin haka za a iya aikata abinda za a yi wa dana sani daga baya a wannan lokaci.

Vincent ya fadi haka ne bisa ga sakamakon binciken da ya gudanar kan dangartakar yunwa da yanke hukunci a jikin wasu daliban jami’ar guda 50.

Ya kara da cewa a duk lokacin da mutum ke jin yunwa zai rika samun gajartar hakuri, yawan fushi sannan zai yi ta yin tunane-tunane haka kawai babu gaira babu dalili.

“A takaice dai sakamakon binciken ya nuna cewa duk mutumin dake jin yunwa zai rika rashin zurfin tunani, fushi ko kuma rashin hakuri da hakan zai sa ba zai yanke duk wani muhimmin shawara akan wani abu ba yadda ya kamata, sai kaga an fada cikin matsala bayan haka.

“Misali mafi yawan mutane kan salwantar da albashin su ko kuma wasu kudade da suka samu saboda a lokacin da suka samu kudaden yunwa ta galabaitar dasu kuma kwakwalwar su ya toshe saboda yunwa sai su rasa me suka yi da kudaden bayan haka.

A karshe dai wannan likita ya yi kira ga mutane da su rika cin abinci a lokaci-lokaci sannan su tabbata cikin su a dame yake tam da tuwo ko abinci kafin su yanke wani shawara akan ko wani irin abu da suka sa a gaba ko kuma suke yi.

” Wannan shine mafita ga mutane. A rika neman abinci akai akai, sannan a hakura da daukar matsaya akan abu idan bulaliyar kan hanya ta fara jidan mutum.

Share.

game da Author