KADUNA: ’Yan sanda sun samu yara sama 300 daure da ankwa a gidan horas da kangararru

0

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kaduna, ta bayyana ceto mutane sama da 300 a wani gidan horas da kangararru da ke tsare sama da watanni uku kowanen su.

Yawancin wadanda aka samu a gidan sun a daure ne da ankwa. Akwai kuma masu tabo a jikin su, mai nuna cewa an rika azabtar da su.

Yan sanda sun ce an fake da nuna cewa gidan makarantar Islamiyya ce da kuma wurin ladabtar da kangararrun yara. Wani mutum ne mai suna Ismaila Abubakar, mai shekaru 39 ke shugaban gidan.

Kakakin ‘Yan Sandan Kaduna, Yakubu Sabo, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa sun kai ziyara gidan jiya Alhamis bayan samun rahoton abin da ke faruwa a gidan.

Sabo ya ce sun damu yara kanana da manya a gidan har masu kimanin shekaru 10. An kuma gano cewa dukkan wadanda ke daure a gidan, iyayen su ne suka kai su, domin a ladaftar da su daga lalacewar tarbiyyar da suka afka.

Ya tabbatar da cewa wurin makaranta ce kuma wurin ladabtar da yara.

“Kwamishinan ‘Yan Sanda da kan sa ya ja tawagar manyan jami’an sa suka je har gidan suka gane wa idanun su. Ya ce abin abin dai shi ne da ba su da rajista.

“Lokacin da mu ka je gidan mun samu yara sama da 300, wasun ma matasa ne ‘yan shekaru 18.

An tambayi abin da ake koyarwa a wurin, sai aka ce wai karatun Arabiya ake koyar da su, kuma kawo kangararru a gidan ana ladabtar da su ta hanyar tsare ko ko daure su.

Gidan dai babu wata sahihiyar hanyar tsarin bai wa yaran ilmi, kuma mai gidan ba masanin matsalar halayyar dan Adam ba ne.

Tuni dai kwamishinan ‘yan sanda ya sa aka fitar da su daga gidan.

An kama mutane bakwai masu kula da gidan da kuma shugaban su.

Share.

game da Author