Shugaban asibitin Barau Dikko dake Kaduna Abdulkadir Tabari ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da malaman makarantun horas da likitoci da su inganta darussa da karin likitoci domin kawar da matsalolin karancin likitoci da ake fama da shi a kasar nan.
Tabari ya fadi haka ne a taron gangami na kungiyar likitocin Najeriya NARD da aka yi a garin Kaduna ranar Alhamis.
Ya ce karancin likitoci da ake fama da shi a kasar nan ya samo asali ne a dalilin rashin inganta makarantun horas da likitoci a kasar nan da a dalilin haka ya sa dalibai da kwararrun likitoci ke ficewa zuwa kasashen waje.
Tabari ya ce sakamakon binciken da WHO ta gudanar ya nuna cewa rashin inganta makarantun horas da likitoci ya sa ake samun kwararrun likitoci akalla 0.37 daga cikin mutane 1000 a kasar nan.
Sannan kungiyar likitocin hakora na Najeriya (MDCN) ya bayyana cewa likitoci 72,000 suka yi rajista da kungiyar wanda daga ciki 35,000 ne ke aiki a Najeriya.
“Hakan na nuna cewa likita daya ne ke duba marasa lafiya 5,700 a kasar nan a maimakon likita daya ya duba marasa lafiya 600 bisa ga tsarin WHO.
“A lissafe Najeriya na bukatan karin likitoci 290,000 idan har ana so a samu gagarimin nasara a fannin kiwon lafiya a kasarnan.”
Tabari ya yi kira ga kungiyoyin ma’aikatan kiwon lafiya da su hada hannu da gwamnatocin jihohi domin gina makarantu da asibitocin horas da likitoci.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da na jihohi da su hada karfi da karfe da hamshakan ‘yan kasuwa na Najeriya domin samar da ingantattun kanyan aiki a asibitocin kasarnan.
Discussion about this post