Gwamnatin Kogi ta kashe Naira biliyan 4 wajen gina masana’antar sarrafa shinkafa

0

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya bayyana cewa jihar ta kashe Naira biliyan hudu wajen gina masana’antar sarrafa shinkafa a jihar da ke iya sarrafa ton 50 na shinkafa a rana.

Gwamna Bello ya fadi haka ne a ziyarar gani da ido da ya kai masana’antar da aka gina a kusa da dam din Omi a kauyen Ejiba karamar hukumar Yagba ta yamma.

“ Dama can mun fadi cewa zamu gina wannan masana’anta sai gashi yau Allah yayi an kammala wanda idan da za a yi nazari kadan za agane cewa gwamnatocin PDP a baya basu iya gina irin wannan kamfani ba atsawon mulkinsu a jihar.

Ya ce masana’antar za ta dauki ma’aikata a kalla 500 kuma duk wata za a samu kudin shiga a asusun jihar da yakai naira miliyan 300 da hakan zai taimaka wa gwamnati matuka wajen samun karin kudaden shiga.

“ Baya ga shinkafa Masana’antar za ta rika sarrafa abincin kifi da kaji domin a kwai akalla mutane masu manyan gidajen kiwon kifi sama da 500 a jihar.

Bayan haka gwamna Bello ya ce gwamnati ta gina kamfanin samar da wutar lantarki da zai iya samar da wuta har wat 500.

“A lissafin da muka yi masana’antar ita kanta za tayi amfani da wat 200 sannan sauran 300 za mu raba wa gidajen dake kusa da dam din.

Ya ce yana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kadamar da wannan masana’anta kafin lokacin zaben gwamnan jihar wato ranar 16 ga watan Nuwamba.

A karshe sarki Kabba Solomon Owoniyi ya yabawa gwamnan bisa gina wannan masana’anta da yayi a yankin su. Sannan yayi kira da a gyara Titin Kabba zuwa Ilori.

Share.

game da Author