‘Yan Najeriya sun kagara su ga an inganta wutar lantarki – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ’yan Najeriya sunn kagara su ga harkar makamashin wutar lantarki ta inganta.

Ya ce kowa na son ganinn karin haske da kuma inganta wutar ta yadda za a rika gudanar da harkokin kasuwanci da ita.

Ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya ke karbar bakuncin Jakadu daga kasar Jamus da kuma Ethiopian, Birgitt Ory da kuma Azanaw Tadasse Abreha.

Buhari ya yi wannan jawabi ne jim kadan bayan ya sanya hannun kulla yarjejeniya da kamfanin Siemens domin inganta wutar lantarki a kasar nan.

Wannan jawabi dai Kakakin Yada Labarai na Buhari, Femi Adesina ne ya fitar da shi.

Kalubale

Duk da dimbin yawan al’ummar da ke Najeriya, sama da milyan 180, har yanzu kasar ta na samar da wutar lantarki wadda ba ta fi ‘cikin cokali’ ba. Tare da wannan kuma akwai matsalolin kula da bangaren lantarkin.

Bayan kulla yarjejeniyar, Buhari ya sha wa jakadar ta Jamus alwashi da daukar alkawarin cewa Najeriya ba za ta karya wannan yarjejeniya ba.

Daga nan ya kara gode wa kasar Jamus saboda irin gudummawar da ta ke bayarwa a bangaren kula da masu gudun hijira a Arewa maso Gabas.

Sannan kuma ya ce ziyarar da Shugabar Jamus, Angela Mikel ta kawo Najeriya, cikin Agusta, 2018 ta kara karfafa dangantaka da diflomasiyyar da ke tsakanin kasashen biyu.

A na ta bayanin, Jakadar ta Jamus ta ce abin alfaharin ta ne da ta ke jakadanci a Najeriya, kasar da ta kira mafi girma da kasaita a Afrika baki daya.

“Lokacin da na zo Najeriya cikin watan Mayu, farkon sauka ta jirgin sama a Abuja, shi ne farkon taka kafa ta Afrika a karo na farko. Ina sauka na ce to ni fa na ga wurin zama na yi aiki.”

Daga nan sai ta taya Najeriya murnar samun manyan matsayi biyu a Majalisar Dinkin Duniya. Wato Mataimakiyar Sakataren Majalisa, Amina Mohammed da kuma Shugaban Zauren Majalisa, Mohammed Bande.

Share.

game da Author