Nuhu Vile na ma’aikatar kiwon lafiyar na jihar Gombe ya bayyana cewa mutane uku sun kamu da zazzabin shawara a jihar.
Vile yace an gano haka ne bayan gwajin mutane shida da aka yi bayan zaton na ko sun kamu da cutar.
Vile ya ce mutane uku din da ake da tabbacin sun kamu da cutar sun samu sauki domin har an sallame su a asibiti.
Ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa cutar ta bullo daga dajin Yankari ne dake jihar Bauchi.
“Mun kuma aika da ma’aikatan mu domin dakile yaduwar cutar.
Vile ya yi kira ga mutane da su daina jira har sai cutan ya galabaitar da su kafin a zo asibiti, yin irin wannan jinkira na iya yin ajalin mutum.
Bayannan ya yi kira ga mutane da su rika tsaftace muhalli, a garzaya da yara wuraren yin allurar rigakafi a lokacin da ya kamata.
Idan ba a manta ba a cikin wata na Satumba ne gwamnatin tarayya ta sanar da hada hannu da kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO, Gavi da ‘Vaccine Alliance domin yi wa mutane miliyan 1.6 allurar rigakafin cutar shawara a jihohi uku na kasar nan.
Allurar rigakafin zai gudana ne a kananan hukumomi uku a jihar Ebonyi, biyu a jihar Benuwai sannan daya a Cross Rivers.
Sannan ‘yan watanni tara zuwa masu shekaru 44 ne za a yi wa rigakafin.