Tsare mu aka yi a Indiya ba batun warkar da mu bane – Inji El-Zakzaky

0

“Ko a gida Najeriya sun yarda, inda ake tsare da mu sun yarda ba wanda zai duba mu sai likitan da muka zaba, muka yarda. To, amma ga shi a nan mun fahimci cewa su likitocin da suka ba mu shawarar a zo nan din sam ba su da ta cewa. Sun ma gaya mana da mu ka yi magana da su, lallai sai dai su zo su bada shawara kawai.”

Jagoran na ‘yan Shi’a a Najeriya, ya ci gaba da nuna takaicin irin abin da aka yi musu a Indiya da masaniyar Najeriya cewa:

“Amma wannan asibitin ke da iko ya zabi duk abin da ya so. Sai na ce masu to, ai bisa aminci ne muka zo, ba zai yiwu kuma mu ga wani likitan da ba mu sani ba, ba mu amince da shi ba ya zo. Kuma wadanda muka aminta ba su shaida mana wani abu game da shi ba ya taba mana jiki, don kada a yi abin da aka so a yi wanda harsashi bai yi ba, a yi shi ta wata hanya.

ZARGIN MAKARKASHIYA: El-Zakzaky ya nemi dawowa Najeriya daga Indiya

“Saboda haka, muna ganin dai gaskiya abubuwan da muka gani a nan ya nuna mana cewa ba mu cikin aminci sam. Kawai an kawo mu wani wuri ne aka tsare.

“Ni an tsare ni shekara yau goma sha uku (13) amma ban ta6a ganin tsaro irin wanda aka yi mini a nan ba. Hatta a kofar dakin da mu ke, ‘yan sanda ne da bindigogi. Hatta kuma ko daki zuwa daki ba a yarda ma mu je ba. Sai na ga cewa to, ni gara ma mu koma a inda nake, duk tsarewar da ake min a Nijeriya ban taba ganin irin wannan ba. Idan an tsare ni a gidan kurkuku akan kulle mu ne karfe tara, a bude mi karfe bakwai na safe. Sannan kuma muna iya zuwa duk inda muka ga dama akalla a eriyar da muke tsare din.

To, amma sai nan na ga ko kirikiri bai kai tsanani a kaina irin wannan ba. To, sai nake ganin cewa to lallai ba zai yiwu mu fito wani kangi domin, mu samu lafiya a dora mu a wani kangi, a kuma mika jikin mu ga wadanda ba mu aminta ba.

A maida mu Najeriya mu nemi magani a wata kasar

“Saboda haka muna tunanin Insha Allahu dai gaskiyar magana ita ce akwai bukatar mu koma gida tunda dai an yarda mu je wani wuri a waje domin magani. Tunda Indiya lallai ba ta zama wurin aminci ba yanzu yanzu a gare mu. Sai dai mu koma gida. Daman akwai wadansu kasashe da suka yi tayi na cewa za su karbe mu idan mun je. Daga ciki akwai Malesiya da Indonesiya da Turkiyya. Sai mu je mu tattauna a zaii daya daga ciki. Sai mu je can Insha Allahul Azeem.”

Share.

game da Author