1 – “Yanzu mu na birnin Delhi ne a Indiya. Kamar yadda dai aka sani an yi shiri na a zo nan domin, bidar lafiya na warkar da wasu matsaloli da muke tare da su, ni da Malama Zeenah. Ita Malama Zeenah akwai cikakken harsashi a jikinta, sannan kuma bayan haka nan akwai bukatar canjin kokon gwiwowinta guda biyu da kuma wasu matsaloli.
2 – “Ni kuma akwai buraguzan harsasai wanda suka farfashe, ‘yan kanana a idanu na da kuma wasu a hannu na, da kuma wasu a cinya ta ta dama wadanda su ne suka rinka yin aman guba, wanda ya sabbaba matsaloli.
3 – “Wadanda daga baya muka gano su ne suka sabbaba mini wannan shanyewar wani barin jiki, na farko da na biyu.”
4 – “To muna tunanin abin da ya kamata a yi na farko shi ne a kwashe wadannan harsasai, wanda yin wannan aikin ba za a iya yi a gida ba, kuma likitoci suka ce a je waje inda ya kamata a yi.
5 – “To, wannan duk mu na murnar cewa idan mun zo nan Delhi za mu samu asibitin da ya dace domin, a yi wannan aiki. To, kuma cikin likitocin da suka zo wajen mu, ko in ce su ka je tunda ba muna a Najeriya ba ne. Su ka je wajen mu a Najeriya su ne suka ba mu shawarar wannan asibiti da ake ce ma MEDANTA. To, kuma shi ya sa ma mu muka nemi a kawo mu nan asibitin din.
6 – “To, tun kafin a kawo mu wanda kuma muna gida muka ji labarin cewa, ofishin jakadancin Amerika ya sa tsama a kan wannan asibiti, kan cewa kada su karbe mu idan mun zo, kuma har sun ce ba za su karbe mu ba.
7 – “Sai mu na tunanin a je wani wuri, idan aka zo din. To, daga baya sai aka ce mana an warware wannan matsalar yanzu sun yarda. Shi ke nan sai muka kamo hanya.
8 – “Mu na isowa mu ka samu tariya na su ma’aikatan asibitin, tun daga filin jirgin sama har zuwa asibiti din. Tun muna cikin motar daukar marasa lafiya su ka ba mu labari na cewa, ainihin akwai mutanen da su kai dafifi a filin jirgin sama domin su gan mu a lokacin da za mu shiga motar. Amma sai suka yaudare su, suka ajiye mota guda biyu a gaban su da cewa a nan za mu shiga, amma sai suka dauke mu a wata motar, suka fita da mu.
9 – “Saboda haka mutanen da su ka yi dafifin sam ba wanda ko da ya hango mu ma. Sannan kuma su ka ce har wala yau mutane a asibiti sun yi dafifi don su ma su ga shigar mu asibiti. Shi ma sai suka ce, amma idan muka je za a shiga ta kofar baya ne. Suka ce sun yi haka ne saboda yawan mutanen nan mai yiwuwa su yi abin da suka ce da Ingilishi su yi “mobbing” din mu, shi ne mutane su na kokarin ko su taba mutum, ko sauran su ya zama wani abu, haka dai suka ce.
10 – “Saboda haka sai muka ga kawai an kawo mu ne wani wurin tsaro, wanda ya fi tsanani ma a kan wanda muke ciki a Najeriya. Sai ya zama suka shigo da ‘yan sanda da bindigogi, sannan kuma da ma’aikatan ofishin jakadancin Nijeriya da yawa. To, kuma dai sai muka lura cewa ainihin an kawo mu wani kangi ne, wanda daman asalin abin a kan aminci ne.
11 – Ko a gida Najeriya sun yarda, inda ake tsare da mu sun yarda ba wanda zai duba mu sai likitan da muka zaba, muka yarda. To, amma ga shi a nan mun fahimci cewa su likitocin da suka ba mu shawarar a zo nan din sam ba su da ta cewa. Sun ma gaya mana da mu ka yi magana da su, lallai sai dai su zo su bada shawara kawai.”
12 – “Amma wannan asibitin ke da iko ya zabi duk abin da ya so. Sai na ce masu to, ai bisa aminci ne muka zo, ba zai yiwu kuma mu ga wani likitan da ba mu sani ba, ba mu amince da shi ba ya zo. Kuma wadanda muka aminta ba su shaida mana wani abu game da shi ba ya taba mana jiki, don kada a yi abin da aka so a yi wanda harsashi bai yi ba, a yi shi ta wata hanya.
13 – “Saboda haka, muna ganin dai gaskiya abubuwan da muka gani a nan ya nuna mana cewa ba mu cikin aminci sam. Kawai an kawo mu wani wuri ne aka tsare.
14 – “Ni an tsare ni shekara yau goma sha uku (13) amma ban ta6a ganin tsaro irin wanda aka yi mini a nan ba. Hatta a kofar dakin da mu ke, ‘yan sanda ne da bindigogi. Hatta kuma ko daki zuwa daki ba a yarda ma mu je ba. Sai na ga cewa to, ni gara ma mu koma a inda nake, duk tsarewar da ake min a Nijeriya ban taba ganin irin wannan ba. Idan an tsare ni a gidan kurkuku akan kulle mu ne karfe tara, a bude mi karfe bakwai na safe. Sannan kuma muna iya zuwa duk inda muka ga dama akalla a eriyar da muke tsare din.
15 – To, amma sai nan na ga ko kirikiri bai kai tsanani a kaina irin wannan ba. To, sai nake ganin cewa to lallai ba zai yiwu mu fito wani kangi domin, mu samu lafiya a dora mu a wani kangi, a kuma mika jikin mu ga wadanda ba mu aminta ba.
16 – “Saboda haka muna tunanin Insha Allahu dai gaskiyar magana ita ce akwai bukatar mu koma gida tunda dai an yarda mu je wani wuri a waje domin magani. Tunda Indiya lallai ba ta zama wurin aminci ba yanzu yanzu a gare mu. Sai dai mu koma gida. Daman akwai wadansu kasashe da suka yi tayi na cewa za su karbe mu idan mun je. Daga ciki akwai Malesiya da Indonesiya da Turkiyya. Sai mu je mu tattauna a zaii daya daga ciki. Sai mu je can Insha Allahul Azeem.”
Haka El-Zakzaky ya rufe bayanin sa.