Jami’an Kwastan sun gano wani dakin ajiya cike fam da Tramadol da Kodin

0

Hukumar kwastam dake kula da shiyar Zone A a jihar Legas ta gano wurin boye miyagun kwayoyi a jihar.

Shugaban kula da shiyar Usman Yahaya ya bayyana cewa sun gano wannan wuri ne a a titin Mile-Oshodi ranar Juma’a bayan kama wata babbar mota dankare da miyagun kwayoyi.

“Mun kama motar ne ranar 13 ga watan Agusta da karfe 2 na dare sannan a binciken da muka gudanar mun gano cewa motar zata je ta ajiye wannan kwayoyi ne a wani wurin ajiya.

“A lissafe dai kwayoyin da muka taras a wannan wuri ya kai na akalla Naira miliyan biyar.

“Akwai kwayar Tramadol katan-katan, kodin da dai sauran miyagun kwayoyi a wannan wuri sannan duka kwayoyin basu da rajista da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC).

Yahaya yace bayan hukumar ta kammala gudanar da bincike za a kone wadannan kwayoyi.

Ya yi kira ga mutane da su rika taimaka wa hukumar da bayanai domin samun nasara akan aikin hana shigowa da miyagunbkwayoyi kasarnan.

Share.

game da Author