A wasan farko na Laliga da aka buga a daren Juma’a Kungiyar Barcelon ta sha kashi a hannu. Bilbao.
Bilbao ta zura kwallon ta daya tal mai ban haushi a ragar Barcelona a daidai minti 89, wato saura minti daya kacal a tashi wasa.
Rashin fitaccen dan wasan kungiyar Barcelona Leo Messi ya nuna karara A wasan.
Barcelona sun yi iya kokarin su su ramo wannan kwallo duk da kara minti uku da akayi bayan cikan lokaci amma ina, hakan bai yiwu ba.
Sabon dan wasan Barcelona, Griezemenda De Jong bai sa kungiyar ta iya fidda kanta daka kunyar da ta shiga a wasan ta na garko a wannan kakan kwallo na Laliga.