RANTSAR DA MINISTOCI: Abubuwa 7 da mai kara yake son Kotu ta yi a kan Buhari

0

1 – Kotu ta hana rantsar da sabbin ministoci.

2 – Ko da an rantsar da su, kotu ta bayyana cewa haramtattun ministoci ne.

3 – Kotu ta yanke hukunci, shin kaffarar rantsuwar kwansitushin ta kama Buhari ko ba ta kama shi ba?

4 – Shin Buhari ya rantse da kwansitushin cewa zai bi doka ko bai rantse ba? Idan ya rantse, to ya karya doka da ya ki nada dan asalin yankin Abuja minista ko bai karya ba?

5 – Shin idan wanda ake kara na farko, wato Shugaba Muhammadu Buhari ya karya wannan dokar, ya cancanci zama shugaban Najeriya ko kuma ci gaba da mulki, ko kuwa bai cancanci ci gaba da kasancewa shugaban kasa ba?

6 – Idan bai cancanci ci gaba da shugabanci ba, mene ne makoma? Idan mai irin wannan karya doka ya ci gaba da mulki, kuma mene makoma?

7 – Kotu ta yanke hukunci idan yankin Abuja, FCT ya cancanci a biya shi diyyar tauye masa hakki da aka yin a tsawon shekaru masu yawa, tun daga 1999.

Sai dai kuma Mai Shari’a Taiwo Taiwo ya kori korafin cewa a haramta tantancewar da Majalisar Dattawa ta yi wa Ministocin.

Sannan kuma ya sa ranar 19 Ga Agusta, wato Litinin mai zuwa zai yanke hukuncin sauraren karar ko kuma a yi watsi da ita.

Share.

game da Author