HAJJI 2019: Akalla Alhazai biyar ‘yan Najeriya ne suka rasu a kasar Saudi

0

Shugaban kiwon lafiyar Alhazan Najeriya na hukumar NAHCON, Ibrahim Kana ya bayyana cewa Alhazai biyar ‘yan Najeriya sun rasu a kasar Saudi.

Kana ya sanar da haka ne ranan Talata inda ya kara da cewa daga cikin Alhazai biyar din da suka rasu akwai mata uku, sannan biyu maza ne.

Da ya rasu a Madina ne sauran kuma a Makka.

“Mun aika da marasa lafiya 108 wadanda ciwon su ya fi karfin mu zuwa asibitoci a madina da Makka.

Kana ya yi kira ga duk Alhazai da su nisanta kansu da inda rakuma suke domin kare kan su daga kamuwa da cutar da ake kira ‘Middle East Respiratory Syndrome Corona Virus (MERS-CoV)’.

“ Ina kuma kira ga duk Alhazan Najeriya da su rika garzaya wa asibitocin mu domin a duba su kyauta. Mun bude su a Makka da Madina da zaran basu jin dadi.”

Share.

game da Author