Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta yi kokarin ganin lallai ta kammala dikkan ayyukan da ta fara, za za a bar kwantai na wani aikin da ba’a kammala ba nan zuwa karshen wa’adin mulkin sa.
Buhari ya yi wannan jawabi ne kamar yadda Kakakin Fadar Shugaban Kasa, Femi Adeshina ya sanr a cikin wata sanarwar da ya sa wa hannu.
Adeshina ya ce Shugaba Buhari ya yi jawabi lokacin da ya karbi tawagar Basaraken Warri, wato Olu na Warri, Mai Alfarma Ogiame Ikenwoli a Fadar Shugaban Kasa, jiya Laraba.
Buhari ya ce gwamnatin sa na daukar matakan da za su kawo karshen matsalar tsaro. Sannan kuma ya na sane da cewa inganta ayyukan raya kasa domin habbaka rayuwar al’umma shi ne abu mafi muhimmanci ga samun ci gaba.
Da ya ke maida amsa a kan gudummawar da kabilar Itsekiri suka ba shi wajen mara masa baya a lokacin zaben 2019, Buhari ya ce “Ina da adadin kuri’un da kabilar Itsekiri suka ba ni, kuma ina sane da kokarin da suka yi min.”
Tun da farko basaraken ya shaida cewa ya je fadar ne domin ya taya Buhari murnar sake samun nasarar zabe.
Ya yi magana ne ta bakin wani basarake mai suna Brown Mene.
Basaraken ya kuma jinjina wa Buhari dangane da nasarar da ya samu wajen karya lagon matsalar tsaro, musamman karfin da Boko Haram ke da shi a shekarun baya da kuma wajen yaki da cin hanci da rashawa.
Ya kuma nuna farin cikin yadda aka fara yashen ruwan mashigar Escfavos da Kogunan Warri.
Sannan kuma Olu na Warri ya bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta kai daukin magance zaizayar kasa a masarautar sa.
Da ya ke magana da manema labarai bayan ya fito daga taron ganawa da Shugaban Kasa, Olu na Warri ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta ci gaba da hobbasan da ta ke yi wajen samar wa matasa ayyukan dogaro da kai, yadda za a hana su afkawa cikin aikata manya da kananan laifuka.
Discussion about this post