Gwamnati ta samar da Naira biliyan 12.7 wa hukumomin kiwon lafiya uku a kasar nan

0

Ma’aikatar kiwon lafiya ta tarayya ta samarda Naira biliyan 12.7 wa hukumomin kiwon lafiya uku a kasar nan.

Ma’aikatar ta bada wadannan kudade ne daga cikin wani kaso da gwamnati ta ware domin inganta kiwon lafiya a Najeriya.

Shugaban shirye-shirye na kungiyar ‘Africa Health Budget Network (AHBN) Aminu Magashi ya sanar da haka da yake ganawa da manema labarai a Abuja.

Idan ba a manta ba bisa ga dokar kiwon lafiya gwamnatin Najeriya ta yarda ta ware kashi daya daga cikin kasafin kudin na duk shekara domin inganta kiwon lafiya.

Tun da aka kafa dokar a 2014 gwamnati bata fara amfani da ita ba sai a 2018 inda ta ware Naira biliyan 12.7 domin rabawa hukumonin kiwon lafiya.

Sai dai kuma a lokacin jihohi 14 ne suka iya cika sharuddan samun wannan tallafi.

Bayan haka Magashi ya bayyana cewa tun a ranar 17 ga watan Mayu ne wadannan kudade suka shiga asusun ma’aikatar kiwon lafiya sannan nan ba da dadewa ba za ta samar da sauran kashi 25 din da ya rage.

Jimmalar kudaden da gwamnati ta ware domin asibitocin sun kai Naira biliyan 55.

“ Daga cikin Naira biliyan 12.7 hukumar inshoran kiwon lafiya (NHIS) za ta karbi Naira biliyan 6.5, hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko (NPHCDA) za ta karbi Naira biliyan 5.8, sannan hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta karbi Naira miliyan 327”.

Magashi ya yi kira ga wadannan hukumomi da su tabbata sun yi aikin da zai inganta kiwon lafiyar mutanen kasarnan.

“Ku fa tuna cewa gwamnati ta ware wadannan kudade ne domin inganta kiwon lafiyar mutane musamman talakawa domin haka ya kamata a rika yi wa mutane bayanin yadda aka kashe wadannan kudade wajen yi musu aiki.

Share.

game da Author