Gwamna Aminu Masari na Jihar Katsina ya bayyana cewa gwamnonin Arewa sun yi wa barayin shanu da ‘yan bindiga afuwa, a wani tayin kokarin da ake yin a samun zaman lafiya a Arewacin Najeriya.
Masari ya yi wannan jawabi ne a cikin wata takardar bayan taro na kwana daya da gwamnonin Arewacin kasar nan suka gudanar a Katsina.
An yi taron ne tare da jami’an tsaro na bangarori daban-daban da ‘yan bijilante sa sauran kungiyoyin sa-kai, makiyaya da kuma manoma, duk jiya a Katsina.
“Daga yau babu wani dan bijilante da ko dan sa-kai da zai kara kai wa Fulani makiyaya hari ko kashe su haka kawai.
“Wannan sadaukarwa kuwa dukkan bangarorin biyu ne za yi ta domin a samu dawwamammen zaman lafiya.” Inji shi.
“A kyale makiyaya da iyalan su su rika zirga-zirgar su sun a shiga kasuwanni da wuraren ibada, ba tare da cin zarafin su ba, matsawar dai ba dauke su ke da makamai ba.
“Maharan da suka saci shanu a cikin kauyuka, to gaggauta maida su ga hannun hukuma ko kuma ga Miyetti Allah.
“’Yan bindiga su damka makaman su da kuma dukkan wadanda suka yi garkuwa da sub a da bata lokaci ba.
“Mu na murna da ganin an saki wasu da aka yi garkuwa da su da dama a Jihar Zamfara da sauran wasu jihohi.” Cewar Masari.
Masari ya kara da cewa jihohi za su yi kokarin ganin an maida himma wajen gina ababen more rayuwa da za su yi wa Fulani makiyaya amfani, kamar asibitoci, makarantu, wuraren kiwo da da sauran su.
A na sa bayanin shi kuma Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ce jihohi za su samar wa Fulani wuraren kiwo domin su samar damar zama wuri daya su na kiwon su.
Ya ce wannan matsaya ce guda daya aka dauka daga bangaren dukkan gwamnonin jihohin kasar nan, domin a daina kashe jama’a haka nan.
“Ku saki dukkan wadanda ku ka yi garkuwa da su, domin ku nuna wa duniya cewa lallai kun tuba, kuma kun daina.”
Shi kuwa Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya yi gargadin cewa kada wani dan bijilante ko dan sintiri ya kara kashe wani mutum da sunan sintiri ko bijilane.
Ya ce duk wanda aka kama ya kashe wani, to za a hukunta shi daidai da laifin da ya aikata.
Su ma Fulani masu hare-hare da garkuwa, su daina, domin duk wanda aka kama zai fuskanci tsatstsauran hukunci.