A safiyar yau Talata ne jami’an EFCC suka kai farmaki gidan tsohon gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode.
Sun kai farmakin ne a ci gaba da binciken harkallar cin hanci da rashawa a EFCC din ke zargin sa.
PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa EFCC ta na binciken tsohon gwamnan, kamar yadda kakakin hukumar Tony Orilade ya tabbatar wa wannan jarida.
An fara binciken Ambode ne watanni kafin saukar sa daga mulki a ranar 29 Ga Mayu, 2019.
An kai farmakin ne a gidan Ambode wanda ke garin su, Epew, wajen karfe 9:35 na safe.
Haka nan an shiga gidan tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Legas, wanda gari daya gidan na sa ya ke da gidan Ambode. Kuma su na makwabtaka da juna.
Ana zargin an karkatar da bilyoyin nairori a zamanin mulkin Ambode.
Ko a cikin makonni biyu da suka gabata, EFCC ta kulle wasu asusun bankuna masu cike da bilyoyin kudade, wadanda aka danganta da cewa duk da sunan Ambode ba ne mai asusun ajiyar, to ya na da alaka da su da kuma kudaden da ke ciki.
Sai dai kuma Ambode ya karyata, kuma ya nesanta kan sa da asusun da kuma dukkann kudaden da aka ce su na cikin su.
Discussion about this post