RASHIN INGANCI: Gwamnatin jihar Ekiti ta rufe asibitoci biyar

0

A makon da ya gabata ne gwamnatin jihar Ekiti ta rufe wasu asibitoci har guda biyar da ke aiki a fadin jihar.

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Mojisola Yaya-Kolade ne ya sanar da haka a lokacin da ya halarci zaman kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa domin bankado baragurbin asibitoci a jihar.

“Gwamnati ta yi haka ne domin ceto rayukan mutanen jihar daga aiyukkan baragurbin likitoci da asibitoci a jihar sannan muna tabbatar wa mutane cewa gwamnnati za ta dauki mummunar mataki akan duk wanda aka kama yana kafa ire-iren wadannan asibitoci.

“Ina kuma kira ga mutane da su guji zuwa asibitocin da basu da lasisi ko kuma suke aiki ba tare da gwamnati ta basu damar yin haka ba.

Yaya-Kolade yace kwamitin za ta ci gaba da aiki tukuru wajen ganin ana bankado ire-iren wadannan asibitoci a w
jihar.

Asibitocin da aka rufe sune, asibitin Omole, asibitin Adedamola, asibitin Divine da asibitin Maternity Home.

Idan ba a manta ba a watan Yuni ne kungiyar masana magunguna na kasa (PCN) ya rufe manya da kananan shagunan siyar da magani 231 a jihar Nasarawa.

Matsalolin da ya sa PCN ya rufe wadannan shaguna sun hada da rashin tsaftace muhalli, rashin lasisi, rashin sabunta takardun da wa’adin su ya kare, siyar da jabun magunguna da rashin kwararren masanin magani a shagunan.

Share.

game da Author