Tsohon Mataimakin shugaban Kasa Namadi Sambo ya karyata shafukan dake yada wasu zantukan karerayi cewa wai yana mara wa masu shirya yi wa gwamnatin Buhari bore.
Namadi yace bashi bane ke da mallakin wadannan shafuka da ke yada irin wadannan kalaman batanci game da gwamnatin Buhari.
Ya kara da cewa ba zai yi kasa-kasa ba wajen ganin an taso keyar masu yada irin wadannan jita-jita da sunan sa domin ayi kyakkyawar hukunta su.
“Ban taba yin amfani da shafukan sada zumunta na zamani ba ballantana in wallafa wani bayani ba, saboda haka duk wani bayani mai dauke da sunana a shafukan sada zumunta na FACEBOOK karya ce kuma ba daga gareni bane”
Sanarwar taci gaba da cewa” Zanyi amfani da wannan damar in jawo hankalin jama’a cewa duk bayanan da ake wallafawa a shafukan sada zumunta na FACEBOOK da sauransu bani bane, hasalima sunayin haka ne domin haifar da rudani da kuma kawo rashin kwanciyar hankali.”
“Marasa kishi da nuna son rai suke yunkurin bata min dangantaka na domin cimma bukatarsu na son rai”Inji Namadi Sambo.
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, ya bayyana cewa baya shiga shafukan sada zumunta na FACEBOOK da sauransu, akan haka, ya bukaci daukacin al’ummar kasar nan da su kauracewa karanta duk wani bayani wanda aka sanya sunanshi a shafukan sada zumunta na zamani suna isar da wasu sakonni na son rai.
Ya ci gaba da cewa. “Na dauka matakai akan irin wadannan shafukan ta Mahukunta shafukan FACEBOOK domin gano wadanda suke daukar nauyin shafukan, haka kuma na sanar da jami’an tsaro su sanya ido akan masu amfani da sunana a shafukan sada zumunta na FACEBOOK domin gurfanar da su a gaban hukumar” a ta bakin Namadi.
Akan hakan, ya bukaci daukacin al’ummar Najeriya da su kaucewa yada labaran karya da sunan wasu domin kaucewa tada rikici da fitina a Kasa.