Mutane miliyan 10 ne ke zukar ganyen Wiwi a Najeriya – Sakamakon Bincike

0

Kungiyar sa ido kan miyagun kwayoyi da manyan laifuka na majalisar dinkin duniya (UNODC) ta bayyana cewa akalla mutane miliyan 10 ne ke ta’ammali da ganyen wiwi a Najeriya.

UNODC ta bayyana haka ne a taron samun madafa game da illar amfani da miyagun kwayoyi da aka yi a Abuja.

Kungiyar ta kuma bayyana cewa zukar ganyen Wiwi ya zama ruwan dare, domin akalla mutane miliyan 188 ne ke amfani da ita a fadin duniya.

Jami’in UNODC Oliver Stolpe ya bayyana cewa kungiyar su ta gano haka ne a wata binciken da ta yi a 2018.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne Hukumar Hana Sha Da Safarar Kwayoyi, NDLEA, ta bayyana cewa, ta lalata gonakin da ake shuka ganyen wiwi a jihar Osun.

Shugaban Hukumar na Jihar, Samuel Egbeola ya sanar da haka a garin Osogbo.

Da ya ke karin bayani, Egbeola ya ce fadin wadannan gonaki sun kai sun kai fadin filin kwallo har guda 74.

Ya kara da cewa sun gano wadannan maka-makan gonakin ne bayan da wani mai kishin kasa ya kawo musu kwarmaton inda ake noman wiwi din, a Ikeji Affeji cikin jihar.

A karin bayanin sa, ya ce sun kama mutane biyu da aka samu su na aiki a cikin wata gonar. Su na tsare ne inda su ke bada bayanin mamallakan wannan katafariyar gona.

Ya kuma ce sun kama buhuna goma a wani samamen wani wuri daban, wadanda ya ce sun kai nauyin kilogiram 107.

A karshe ya ce ba za su gaji ba wajen kokarin su na ganin sun kakkabe muggan kwayoyi a kasar nan.

Share.

game da Author