Hukumar Kwastan ta kama motan daukar marasa lafiya dankare da kwalayen Taramol

0

Hukumar kwastan dake Apapa a jihar Legas ta kama wata motar daukan marasa lafiya dankare da kantan 10 maganin Tramadol.

Jami’in hukumar dake kula da shiyar Apapa Mohammed Abba-Kura ya sanar da haka da yake zantawa da manema labarai a Legas.

Abba-Kura ya bayyana cewa sun kama wannan mota ne a tashar jiragen ruwa dake Apapa ranar Juma’a da karfe 11 na dare.

Ya ce a lissafe katan 10 na maganin Tramadol da suka kama zai kai akalla Naira miliyan uku.

“ Binciken da muka yi ya nuna cewa shigowa aka yi da wannan mota daga waje sannan daga cikin katan din maganin wanda ke dauke da tambarin kasar India sai da aka cire maganin guda 211.

Abba-Kura yace sun kama mutane biyu da ake zargi suna da hannu a safarar wannan magani.

“ Mun kama Michael Ajibade da Olatunde Emmanuel ma’aikatan kamfanin ‘Medbury Medical Services’ domin yin bincike a kansu.”

Kwanakin baya Jami’in hukumar kwastam na Najeria Jonah Achema ya bayyana cewa hukumar ta kama kwantena 12 dankare da kwayar Tramadol a tashar jiragen ruwan dake Apapa jihar Legas.

Share.

game da Author