SHARI’AR ZABE: Mai Shaida ya zargi ejan din APC da kekketa sakamakon zaben shugaban kasa

0

Wani mai bada shaida a Kotun Daukaka Karar Zaben Shugaban Kasa, ya zargi ejan din APC da laifin kekketa sakamakon zaben Shugaban Kasa a lokacin zaben 23 Ga Fabrairu, a Jihar Bauchi.

Ya’u Yusuf ya na bayar da wannan shaida ce a lokacin da lauyoyi ke yi masa tambayoyi a kotun sauraren karar zaben shugaban kasa wadda Atiku Abubakar da PDP suka kai INEC, APC da kuma Shugaba Muhammadu Buhari, su na kalubalantar nasarar da aka ce Buhari da APC su ka yi.

Yusuf ya shaida wa kotu cewa ya na aiki ne a Karamar Hukumar Dass ta cikin Jihar Bauchi. Ya ce ejan din APC ne ya yi amfani da wata dama ya kekketa sakamakon zabe, a lokacin da aka kirawo jami’an tsaro na JTF su tsare cibiyoyin zabe, bayan tashin bam.

Ya ce ejan din APC ne suka kutsa cikin cibiyoyin zabe suka kekketa sakamakon zaben, sannan suka maye gurbin su da wasu da suka yi harkallar buga da kwamfuta.

Yusuf ya kara da cewa ‘yan sanda ne suka dauki kwafen sakamakon da aka kone, suka yin alkawarin za su binciki lamarin.

“Ejan din APC ne ya kekketa sakamakon zabe na ainihi a gaban jami’in zabe.” Haka Yusuf ya shaida wa alkalai da lauyoyi a cikin kotun, a Abuja.

Da aka tambaye shi ko ya na da masaniyar an yi bincike kuma ko an gurfanar da wani a kotu dangane da batun kekketa sakamakon zaben, sai Yusuf ya ce bai sani ba.

Ya kuma yi zargin cewa a makare aka fara zaben, saboda jami’an zabe sun ki zuwa da wuri.

Masu shaida guda 10 ne suka gabatar da shaidar su a jiya Alhamis. Ya zuwa yanzu PDP ta gabatar wa kotu masu shaida har mutum 29.

Tun farko dai dai PDP ta shaida wa kotu cewa za ta gabatar mata da masu bada shaidar cewa an tafka magudi a zaben shugaban kasa na 2019 domin a bai wa APC nasara, har mutum 400.

Ya zuwa yanzun dai PDP na da sauran kwanaki 5 wadanda za ta gabatar da sauran masu shaidun da za ta iya gabatarwa.

PDP na gabatar da masu shaida ne a kokarin ta na tabbatar wa kotu cewa an tafka magudi a zaben shugaban kasa na 2019.

A yau Juma’a za a ci gaba da sauraren shaidun da PDP ke gabatar wa kotu, kamar yadda Shugaban Kotun Mohammed Garba ya bayyana.

Share.

game da Author