Sai an yi karo-karon naira tiriliyan 10 za a iya wadatar da ayyukan raya kasa -Fashola

0

Tsohon Ministan Ayyuka, Gidaje da Makamashi, Raji Fashola, ya bayyana cewa Najeriya na Bukatar akalla naira tiriliyan 10 kafin ta samu wadata kasar nan da ayyukan raya kasa da inganta al’umma a fadin kasar nan.

Da ya ke jawabi a zauren Majalisar Datttawa a lokacin da ake tantance shi, Fashola wanda a yau Litinin shi ne na farkon tantancewa, ya ce babbar matsalar da kasar nan ke fuskanta ita ce babu wadattun kudaden da Gwamnatin Tarayya za ta gudanar da ayyukan raya kasa da inganta al’umma.

A kan haka ya ce akwai bukatar a zuba asusun hannayen jari da za a iya tara akalla naira triliyan 10 domin a gudanar da ayyukan raya kasa da kudaden.

Tuni dai aka tantance sama da sabbin ministoci 20 kafin yau Litinin, daga cikin sunaye 43 da Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa domin tantancewa.

Fashola ya bada shawarar cewa Majalisar Dattawa ta yi wata doka a kan kafa asusun samar wa wadannan makudan kudade.

Sannan ya ce Najeriya ta mika kokon barar ta ga dukkan mai son zuba jari a asusun. “Ko naira 1,000 ce mai sha’awar zuba jari zai iya sakawa domin tara kudade a wannan tsarin tara kudade na tsarin ‘bond’.

“Babban kalubalen da ke fuskantar gina titina su ne rashin kudaden da za a gudanar da ayyukan da su. A cikin shekaru uku da suka gabata, ya kasance kudaden mu ba su iya isa a gudanar da ayyukan raya kasa da su ba.

“Don haka ni ina ganin cewa akwai wata dama wadda za mu iya yin amfani da ita, ta hanyar fadada shirin gina ayyukan raya kasa, wanda ya yi kamanceceniya da tsarin Sukuk. Mu yi kirdadon cewa mu na bukatar zunzurutun naira tiriliyan 10, wadanda za a iya tarawa ko harhada karo-karon su kashi daban daban. Jama’a duk mai sha’awa zai iya zuba hannun jari ko da na naira 1,000 ne.”

Fashola ya ce gwamnatin tarayya ta dade ta na samun tasgaron kasafin kudi, maimakon a ce ana samun rarar kudade, sai ma gibi ake samu a duk shekara idan aka yi kasafin kudi na shekara.

Ya ce wannan kuwa duk rashin isassun kudade a hannu gwamnati ke haifar da haka din.

Ya nuna cewa tsarin da gwamnati ke bi a lokacin sa, tamkar aikin magudanar ruwa ce, wadda Fashola ya ce amma a halin da ake ciki ga ruwa ya cika, sai dai babu hanyoyin da ruwan zai fice.

Daga karshen Fashola ya shafe lokaci ya na tallata nasarorin da ya ce ya samu a ma’aikatu uku da ya rike lokaci daya, daga 2016 zuwa 2015.

Share.

game da Author