Mahara sun kashe wani shahararren dan Kasuwa a jihar Kebbi, sun yi garkuwa da matarsa da dansa

0

A garin Gulma dake jihar Kebbi ne wasu mahara su ka far wa gidan wani attajiri kuma fitaccen dan kasuwa mai suna Yusuf Garkar-Bore mai shekaru 65 inda suka harbe shi sannan suka yi garkuwa da matarsa Aisha Yusuf da dansa .

Wani makusancin iyalin da baya so a fadi sunan sa ya bayyana haka wa manema labarai ranar Lahadi.

A bayanan da ya yi yace maharan sun far wa gidan Garkar- Bore da karfe 2 na daren Lahadi inda suka harbe shi a kirji.

“ Bayan sun harbe Garkar-Bore a kirji sai suka tasa keyar matarsa da dansa Aisha suka yi awon gaba da su.

“Garkar-Bore ya rasu a dalilin yawan harsashin da suka dirka masa a jika tuni har mun yi jana’izan sa sai dai kuma babu wanda yasan ko wani hali Aisha da dan sa da suka tafi da suke.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Nafi’u Abubakar ya tabbatar da aukuwan haka yana mai cewa rundunar ta fantsama domin ceto wadanda aka yi garkuwa da su.

Garkuwa da mutane ya yi matukar kazancewa a yankin arewacin Najeriya. Domin ko a makon jiya an ruwaito yadda wasu masu garkuwa suka yi garkuwa da darektan kotun daukaka kara na kotun shari’a dake Kaduna da kuma matar sa sannan har suka kashe daya daga cikin ‘ya’yan sa maza.

Share.

game da Author