RASHIN TSARO: Buhari ka tashi tsaye tun kafin wuri ya kure – Emeka Anyaoku

0

Tsohon Babban Sakataren Kungiyar Kasashe Rainon Ingila, wato Commonwealth, Emeka Anyaoku, ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya tashi tsaye ya kawar da dabi’un bangaranci, ya fuskanci yadda zai kawar da kabilanci da addinanci.

Anyaoku ya yi wannan jawabi ne a wurin kaddamar da littafi jiya Talata a Abuja.

Cikin makon da ya gabata dai Buhari ya fuskanci caccaka daga dimbin jama’a dangane da tabarbarewar tsaro.

Cikin wadanda suka caccake shi, har da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, wanda ya rubuta masa budaddiyar wasika, da kuma Wole Soyinka.

“Kafin kowace babbar kasa mai tarin al’umma da kabilu daban-daban ta ci gaba, sai an ja kowane bangare a jika, an gudanar da komai bai-daya, domin kishin ci gaban kasa.”

Haka ya furta a wurin taron kaddamar da littafi wanda masanin shari’a, Dadi Onyeama ya yi a Cibiyar Taro ta ‘Yar’Adu’a, Abuja.

“Akwai batutuwa guda biyu a sha’anin ci gaban zaman tare a matsayin kasa daya al’umma daya. Na farko shi ne kowane bangaren al’umma ya san cewa kuma ya ji a jikin sa cewa an rungume shi ana tafiya tare. Wannan ke kara dankon zumunci da kaunar juna da kishi a tsakanin kowane bangare na al’ummar cikin kasa.

Anyaoku ya yi shugabancin Kungiyar Kasashe Rainon Ingila har tsawon shekaru 10, daga 1990 zuwa 2000. Ya na daya daga cikin mashahuran ‘yan Najeriya da ake mutuntawa kuma ake gani da daraja da martaba.

Ba kamar Obasanjo da Soyinka ba wadanda ke yawan maganganu a kafafen yada labarai dangane da abin da ya shafi gwamnati.

Anyaoku bai cika magana ba, kwata-kwata.

Sai dai kuma a wannan karon, ganin yadda tsaro ke kara mummunar tabarbarewa, musamman garkuwa da mutane, rikicin makiyaya, fashi da makami da hare-haren kashe-kashe da kuma banka wa kauyuka wuta, Anyaoku ya ce ya zama dole ya fito ya shaida wa Buhari gaskiya cewa ya tashi tsare ya yi wa tubkar hanci, tun kafin wuri ya kure.

Musamman Anyaoku ya ce tun farko kamata ya yi a ce Buhari ya yi nazarin abin da ka iya biyo bayan shirin da gwamnatin sa ta so yi, na kafa wa Ruage a kasar nan. Ya ce ba a yi nazarin matsalar tsaron kasar nan kafin a yi niyyar kirkiro shirin ba.

Anyaoku ya ce lokaci na gudu, wuri ya kusa kurewa. Don haka ya kamata hukumomin da abin da ya fi shafa su gaggauta ceto kasar na daga afkawa mummunan bala’i.

A karshe ya ce ko wadanda ke cikin gwamnati sun san akwai matsala a tattare da wannan gwamnatin.

Don haka ya yi kira ga Shugaban Kasa, Majalisar Tarayya, Gwamnoni da sauran wadanda abin ya shafa, su gaggauta ceto kasar nan faga afkawa cikin hargitsin da ka iya hargitsa ta gaba daya.

Share.

game da Author