Tun bayan kasancewar Najeriya a matsayin cikakkiyar kasa, anyi kokari ko ta ina a samar da tsarin gwamnatin tarayya a cikin kasar.
Tsarin gwamnatin tarayya ne ya bayar da dama ga kowane bangare na kasa ya samu wakilci a cikin gwamnati, siyasa da abubuwan yau da kullum ta hanyar bin tsarin ‘federal character’.
Tsarin fedaraliya yana bawa kowane bangare na kasa damar samun wakilci a kowane gurbi na gwamnatin tarayya.
A cikin aikin gwamnati akwai shi, a harkar sana’a da samar da ilimi ga ‘yan kasa akwai shi, ballantana kuma siyasa da take bayyanashi karara.
Mutane suna kurkure wajen kayyade tsarin fedaraliya a iya gwamnatin tarayya. Gaskiya ya wuce don har a karamar hukuma akwai shi saboda mazabu suna da wakilci a ayyukan karamar hukuma.

Misali, idan jiha zata dauki mutane aiki ko zata samar da wani abu don cigaban al’umma dole ne ta rabashi a tsakanin kananan hukumomin da take dasu. Shiyasa zaka samu wasu kananan hukumomin basa iya cike gurbin da aka basu (quota).
A bangaren siyasa kuwa, wannan shahararren abu ne, don duk wanda yake ji kuma yake gani yasan yadda wakilci yake aiki saboda ita gaba dayanta ma wakilci ce.
To meyasa wannan tsarin na fedarilya baya aiki a cikin kungiyar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles?
Amasar da za a iya bayar wa itace, harkar wasan kwallo dama ce ga mai rabo (Privilege) ba ‘yanci ba (Right).
Madallah! Tunda dama ce, yakamata a saketa ga kowane bangare na kasar don a za6i ‘yan kwallo na gaske.
Amma a halin da ake ciki yanzu, a cikin ‘yan kwallon da suke bugawa Najeriya kofin kasashen Afrika (ACON), babu ‘yan Arewa guda shida bayan kuma muna da jihohi sha-tara (19).
Ko za ace babu ‘yan kwallon da za a gwada a yankin ne? Gaskiya babu wannan maganar.
Misali, babu wasu masu wakiltar Arewa idan ka dauke Ahmad Musa da Jamilu Chollins da Shehu Abdullahi, toh sai Mikel Obi da yake wakiltar jihar Plateau wai.
Idan banda rashin kulawa, ai ko a benci an tafi da matasanmu don dai a rufe mana baki. Amma an bar abun a hannun ‘yan kudu maso gabas (Southeast) da kudu maso kudu (South-south). Ita kanta kudu maso yamma (southwest), dan kwallonta daya ne kacal, shine Bolugun.
Idan kuma ance sai wanda yake yin wasa a turai shi kadai za a kira. Wannan gidadanci ne tabbas, to yaushe zaku siyar da yaranku na gida kenan wadanda ake kiransu da home best?
Kuma ai muna da wadanda suke bugawa a kasashen wajen, da yawa daga cikin su an yi watsi da su, ba a ma bi ta kansu ko kuma a san inda suke bugawa ko kuma asan irin gudunmuwar da suke ba kungiyoyin da suke taka tamola a can ballantana a kira su su bugawa Najeriya. Wai shin ko dan ‘yan Arewa ne yasa aka maida su ‘ya’yan bowa?
Laifin su waye a Arewa?
Laifin shugabanninmu ne musamman gwamnoninmu, bamu da hadin kai, bama taimakawa junanmu, mun kyale hassada da qyashi sun yi mana katutu a zuciya. Mutanenmu basu da izza (Confidence), sun bar ‘yan kudu sun fisu izza, manyanmu sun koma amshin shata. Abubuwan da su Sardauna suka gina anata rushesu a Arewa saboda rashin kishin juna.
Menene mafita yanzu?
Dole ne sai an dawo da martabar Arewa ta hanyar taimakon kai-da-kai, kishin juna, neman ilimi da aiki dashi, samun izza da yawaita addu’a da bin doka.
Sannan kuma dole ne sai matasan Arewa sun dage sun ajje lalaci a gefe sannan su kuma manyan yankin sai sun taimakawa wadannan matasa.
Allah ya shiryar damu.
Discussion about this post