Sanata Peter Nwaoboshi da gwamnatin tarayya ta bayar da sanarwar kwace kadarori daga gare shi, ya bayyana cewa gine-ginen da aka manna wa sanarwa kawacewar ba gidajen sa ba ne.
Sai dai kuma Sanatan mai wakiltar Shiyyar Jihar Delta ta Arewa, ya tabbatar da cewa asusun da akwa kulle duk na sa ne.
Ya kalubalanci Shugaban Kwamitin Bincike na Shugaban Kasa, Okoi Obono-Obla cewa ya bayyana wa duniya adadin kudaden da ya ke ta taratsin cewa ya kulle a cikin asusun sa.
Ya ce idan ya sanar, hakan zai sa ‘yan Najeriya su yi hukuncin cewa shin wadannan kudaden sun fi karfin a ce sanata ya mallake su ko a’a.
Haka sanatan mai wakiltar PDP ya bayyana wa Gidan Talbijin na Channels jiya Litinin a Abuja.
“ Dukkan gidajen da su Obla suka sa aka kulle, babu ko daya da na mallaka. Na fada a baya, kuma na sake fada a yanzu cewa ba kadarori na ba ne.
“ Ba ni da ko fegi a Warri, ba ni da ko shagon aski a Lagos, ba ni da ko kwatina a Maitama, Abuja.
“ Ina kalubalantar su Obla da suka sa aka kulle min asusun banki da ya fito ya shaida wa Najeriya ko nawa aka samu a cikin asusu na. Domin su yi shaida shin ko kudin sun fi karfin a ce Sanata ya mallaka ko ba su fi ba.” Inji Owaoboshi.
Ya na magana ce a fusace dangane da wasu kadarori da aka kwace da suka hada da gidaje, gidajen mai da sauran kadarori da aka yi zargin cewa na Sanata Nwaoboshi ne.
An kulle asusun ne da kadarorin guda 14 bayan da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci a kulle su tare da asusun banki 22 da aka yi zargin cewa na sa ne.
Ta ce a kulle su kafin yanke hukuncin da za ta yi tukunna, wato kullewar wuci-gadi, da a Turance aka fi sani da ‘interim forfeiture’.
An zarge shi ne da kantara karya wajen bayyana kadarorin da ya mallaka.