Kungiyar Kwallo Kafan Najeriya, Super Eagles ta yi nasara akan Kugiyar kwallon kafa ta kasar Tunusia a wasan wanda zai zo na uku a gasar cin kofin Nahiyar Afrika.
Lamba 9 Najeriya, Ighalo ne ya jefa kwallo daya tak a ragar Tunisia tun a farkon minti Uku da fara wasa.
Haka aka yi fadi tashi kamar za a ba za a ba har dai minti casa’in din ya cika.
Bayan an kara mintuna 5 bayan cikan lokaci, da ita kanta Najeriyan da Tunisian babu wanda ya iya saka kwallo a ragar wani.
An tashi wasan Najeriya na da ci 1 Tunisia 0.
Za abuga wasn karshe tsakanin Algeriya da Senegal ranar Asabar.
Discussion about this post