Jami’in Hukumar zabe da ke kula da maahajjatan Najeriya a garin Madina ya bayyana cewa daga yau Alhamis, za a fara jigilan ‘yan Najeriya daga garin Madina zuwa Makka.
Ahmed Maigari ya bayyana cewa an baiwa Kamfanin Motoci dake garin Madina kwangilar wannan aiki.
Ya ce akalla mahajjata 35,000 ne daga Najeriya suka isa garin Madina zuwa yanzu domin fara aikin hajjin bana.
sannan kuma za a fara aikin jigilar mahajjatan ne da Alhazai 3,801 daga garin Katsina da Legas.
Zuwa yanzu dai, ana ci gaba da jigilan ‘yan Najeriya daga jihohin Kasar nan zuwa kasar Saudiyya.