Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya roki Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) cewa don girman Allah kada ta sake fusata ta tsunduma yajin aiki, saboda jinkirin fara biyan karin albashi mafi kankanta na naira 30,000 da gwamnatin tarayya ta yi.
Lawan yay i wannan rokon ne jiya Laraba a lokacin da Shugabannin Kungiyar Kwadago na Kasa da na Kungiyar Ma’aikatan Majalisar Tarayya (PASAN), suka kai masa ziyara.
Shugaban kungiyar na kasa Ayuba Waba da Sunday Sabiyi ne suka jagoranci wadanda suka kai wa Lawan ziyara a Abuja.
Shugaban Majalisar Dattawa Lawan, ya kara rokon su da su kai zuciya nesa, su kar fahimtar irin kokarin da gwamnati ke yi, kuma su kara cusa wa zukatan su kishin kasar nan.
Ya ce ya kamata su yi la’akari da cewa akwai jihohin da har sun ma fara biyan tsarin sabon albashin na naira 30,000 mafi kankantar albashi.
“Kada mu rika zuguguta wabi abu na son kan mu ya mamaye nauyin kishin kasar da muke da shi na bai daya, da kuma hakkin da ke kan mu na gina kasautacciyar Najeriya.
“Mu a Majalisa za mu tafi tare da ku domin mu tabbatar da cewa an fara amfani da wannan sabon tsari da gwamnatin tarayya ta amince da shi, na N30,000 mafi kankantar albashi.” Inji Sanata Lawan.”
Ya kuma yi alkawarin yin aiki kafada-da-kafada da kungiyar ma’aikatan majalisar tarayya, wadanda ya ce su rika bijiro da batutuwan da za a rika zaunawa ana bubawa, ana kamo bakin zare, a mimakon gaggawar tafiya yajin aiki.