Ana ci gaba da kara samun baraka tsakanin Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki, da kuma ubangidan sa, Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole.
Oshiomhole ya yi gwamnan Edo tswon shekaru takwas, daga nan kuma ya daure wa Obaseki gindi ya maye gurbin sa.
Jiya Laraba Obaseki ya tsige kwamishinoni takwas wadanda PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa masu biyayya ne ga Adams Oshiomhole.
Wadanda aka tsige din sun hada da Kwamishinan Makamashi Joseph Ugheoke da Harkokin Ruwan Sha, Magdelene Ohenhen Kwamishinar Harkokin Mata. Akwai kuma Osahon Amiolemen na Ayyukan Raya Kasa.
Sauran sun hada da David Osifo na Harkokin Lafiya, Mika Amanokha na Harkokin Matasa da Ayyukan Musamman, Mariam Abubakar ta Kasafin Kudade, Emmamnuel Usoh na Samar da Ayyuka da kuma Christopher Adesotu na Kimiyya da Fasaha.
Tuni har Gwamna Obaseki ya aika wa Majalisa sunayen sabbin Kwamishinonin da za su maye gurabun su, domin majalisar ta tantance su.
RIKICIN GWAMNA DA OSHIOMHOLE
Adamas Oshiomhole ya kammala wa’adin sa na shekaru takwas accikin 2016, kuma ya daure wa Obaseki girndi ya ci zabe a karkashin jama’iyyar APC.
Obaseki na kokarin yin tazarce a zaben gwamnan da za a gudanar cikin 20120, amma kuma alamomi na nuni da cewa a yanzu Oshiomhole ba ya goyon bayan sa.
Rikici a tsakanin su ya fara fitowa fili kwanaki kadan da suka gabata, lokacin da wasu ‘yan majalisar dokokin jihar Edo su tara suka zabei Kakakin Majalisa a cikin dare, kuma suka rantsar da shi.
Majalisar dai ta na da mambobi 24, kuma dukkan su ‘yan APC ne.
PREMIUM TIMES ta gano cewa an gaggauta rantsar da Kakakin Majalisar Jihar ne a cikin dare, domin kada masu goyon bayan Oshiomhole su yi kaka-gida a wurin zaben.
Tuni dai Oshiomhole da uwar jam’iyyar APC ta kasa suka yi watsi da wannan zaben kakakin majalisa na Edo, su na karin bayanin cewa haramtaccen zabe ne.
Tuni dai a jiya Laraba APC a jihar Edo da Majalisar Jihar suka samu amincewa daga Babbar Kotun Tarayya, inda kotu ta umarci uwar jam’iyyar APC ta kasa kada ta shiga cikin sha’anin Majalisar Dokokin Jihar Edo.
Discussion about this post