Hukumar NAQS ta karyata zargin karbar kudade daga masu safarar kayan abinci

0

Hukumar Kiyaye Kamuwa da Cututtukan Dabbobi da Kayan Abici ta Kasa, NAQS, ta karyata zargin da ake wa jami’an ta cewa su na tare masu safarar kayan abinci su na karbar kudade.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na hukumar ya aiko wa PREMIUM TIMES a yau Laraba, Chigozie Nwodo ya bayyana cewa dukkan zarge-zargen da masu sayan da kayan abinci ke yi wa jami’an hukumar karya ce kawai.

Daily Trust ta ruwaito cewa wasu mambobin Kungiyar Masu Sayar da Kayan ABinci ta Najeriya (FSDAN), ta yi barazanar barkewa da yajin aiki, saboda dalilin yawan tare tare mambobin ta da jami’an NQAS ke yi a shingayen bincike su na karbar kudade a hannun su ba bisa ka’ida ba.

Kungiyar kuma ta yi kira da gwamnati ta yi gaggawar cire wadannan shingaye da aka kafa, wanda suka ce ba ya amfana wa kasar nan ko al’umma komai sai dai cutar dilolin kayan abinci kawai da ake yi a wuraren ana kwace musu kudade.

Hukumar NQAS dai ta na karkashin Ma’aikatar Gona da Rana Karkara ce.

Cikin wata sanarwa da Shugaban Kungiyar FSDAN, Christian Afiaonwu ya sa wa hannu, ya ce masu sayar da abinci sun damu kwarai da yawan shingayen da jami’an hukumar NQAS ke kafawa a kan titi barkatai musamman a Jihar Benuwai wadanda da rana kata su ke karbar kudade a hannun dilolin kayan abinci, ba kunya ba tsoron hukuma.

Sun ce shingayen da aka kafa ana tare dilolin kayan abinci a Katsina-Ala da Orokam, duk a cikin Jihar Benuwai, haramtattu ne.

Sai dai kuma cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na hukumar ya aiko wa PREMIUM TIMES a yau Laraba, Chigozie Nwodo ya bayyana cewa dukkan zarge-zargen da masu sayar da kayan abinci ke yi wa jami’an hukumar karya ce kawai.

Ya ce aikin jami’an hukumar ne su rika tare motocin da ke tafiya kan titi a dukkan fadin kasar nan, su na binciken lafiyar kayan abincin da suke dauke, musamman amfanin gona, dabbobi da kayan marmari daga ‘ya’yan itatuwa.

Ya kara da cewa kuma aikin su ne tabbatar da cewa wadannan amfanin gona da dabbobi ba su samu barazanar kamuwa da wata cuta ba.

Sai kuma ya kara da cewa duk wani shingen da aka gani a fadin kasar nan na wannan bincike, ba a kafa shi ba sai da iznin Ma’aikatar Gona da Raya Karkara ta Kasa.

Sannan ya yi karin bayanin cewa duk wata motar da ke fitowa daga Arewacin kasar nan zuwa kudu dauke da akayan abince, ana tare ta ne a yi bincike a bisa yadda doka ta tanadar.

Batun kudaden da aka yi korafin ana karba kuwa, ya ce doka ce ta ce a tika karbar kudaden.

Share.

game da Author