Hukumar kwastan dake kula da shiyar Zone B a jihar Kaduna ta sanar cewa tsakanin watannin Janairu zuwa Yuni hukumar ta kama kayan da ya kai Naira biliyan 1.05 a jihar.
Shugaban hukumar Mustapha Sarkin -Kebbi ya sanar da haka wa manema labarai a garin Kaduna inda ya kara da cewa kamen da hukumar ta yi bana ya zarce bara.
A lissafe dai hukumar ta yi kame sau 623 a tsakain watanni shida da suka gabata sannan a tsakanin wannan lokaci hukumar ta kama motoci 153, buhunan shinkafa 8,168, katan din taliya 820, buhunan siga 167, dila gwanjo 147, jarkunan man gyada 1,035, tayoyin motoci 333 da kwalayen Tramado 1,550.
Sarkin-Kebbi yace sun kuma kama mutanen 14 da suke da hannu a shigo da wadannan kaya inda daga ciki biyu an yanke musu hukunci sannan hudu na jiran kotu ta yanke musu hukunci.
Ya kuma ce hukumar ba za ta yi kasa-kasa ba wajen ganin ta gudanar da aiyukkan ta yadda ya kamata.
” Mun samu labarin cewa masu shigowa da kayan da gwamnati ta hana na amfani da miyagun makamai domin ko a kwanakin baya an kashe mana ma’aikata a jihohin Kano da Katsina amma ina tabbatar muku da cewa hakan ba shine zai karya mana gwiwa ba.”
“ Ina kira ga masu shigo da kaya irin haka da su daina su nemi sana’a ta gari.”
Sarkin-Kebbi ya kuma yi kira ga sauran hukumomi a kasar nan kan mara wa hukumar baya wajen wayar da kan mutane game da illar yin fasakwaurin abubuwan da gwamnati ta hana shigowa da su.