Gwamna Babagana Zulum ya dakatar da Shugaban Likitocin Asibitin Zamani na Umaru Shehu da wasu likitoci hudu.
Hakan ta faru ne a dalilin samun likitocin ba su wurin aikin su, a wata ziyarar bazata ta samamen duba-gari da ya kai wasu asibitoci a cikin dare jiya Talata.
Samamen da ya kai ya biyo bayan yawan korafe-korafen da ake yi cewa likitoci ba su tsayawa sun a kula da marasa lafiya, sai dai su rika fashi sun a tafiya asibitocin su na kan su da suka kafa a cikin Maiduguri.
Dukkan likitocin da aka dakatar din ba su kan aikin su a lokacin da gwamnan ya kai ziyarar bazata din.
An ce lokacin da gwamna ya kai ziyarar bazata a Asibitin Zamani na Umaru Shehu Ultramodern Spacialist Hospital, bai samu yawancin likitocin da ke kan aiki ba, ciki kuwa har da wadanda ya dakatar din.
An ce gwamnan ya sa nas-nas din da ya samu a asibitin ta kira wasu likitoci da nufin su dawo asibitin, amma dukkan su babu wanda ya dauki waya ya amsa kiran da aka yi masa, har lokacin da gwamnan ya fice daga asibitin.
Daga nan sai gwamna ya nemi jin dalilin yadda shi shugaban likitocin ya bar likitocin da ke karkashin sa kowa ya kama gaban sa, ba su tsaya duba marasa lafiya ba.
Sai dai kuma shugaban likitocin ya kasa bai wa gwamna sahihiyar amsa, yay i ta kame-kame.
Kakakin Yada Labarai na Gwamna Zulum, Isa Gusau, ya bayar da sanarwar dakatar da shugaban likitocin da kuma wasu manyan likitoci hudu.
“Gwamna Zulum ya bada umarnin dakatar da Babban Daraktan Lafiya na Asibitin Umaru Shehu, wato Dakta Audu Usman, saboda sakacin rashin iya shugabanci.” Inji sanarwar da Isa Gusau ya fitar.
“Haka an dakatar da Dakta Musa Chuwang da Dakata Chijioke Ibemere, sai kuma Dakta Ali Malgwi.
“Haka ita ma Dakta Easter wadda ya kamata a ce ta na kan bakin aikin ta a ranar da lokacin amma ba ta nan, wannan dakatarwa ta shafe ta.
“An dakatar da Malgwi saboda an kira wayar sa shi ma bai dauka ba, an nemi shi kuma ba ya kusa, duk kuwa da cewa gidan sa a cikin asibitin ya ke.
Sanarwar ta umarci Babban Daraktan Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Barno ya tabbatar da an bi umarnin dakatarwar da Gwamna Zulum ya yi wa likitocin.
Haka nan washe gari ya kai irin wannan ziyara a Sakateriyar Jihar, inda ya sha mamakin yadda ma’aikata ba su fita aiki da wuri ba.