Abdulmumini Jibrin ba bako bane a labban mutanen kasar nan musamman idan ana maganar harkar siyasa da rudanin majalisar tarayya ne.
Idan ba a manta ba Abdulmumini jibrin ne ya zake lokacin da ake neman nada shugaban majalisar Tarayya da ta gabata wanda Yakubu Dogara ya shugabanta. Sai dai kuma tun tafiya bata yi nisa ba suka yi kaca-kaca da shi Abdulmumini da wasu da shugabannin majalisar.
Hakan ya sa ya rika yi wa shugaban majalisar Dogara da wasu ‘yan majalisar tonon silili. Ya rika fitowa da wasu takardu yana bayyana yadda suka rika yin aringizo a kasafin kudin kasa.
Daga bisani majalisar ta dakatar dashi har na kusan shekara biyu.
Haka dai ya ganganda ya samu ya komo a daidai an kusa kammala zangon wannan mulki a wancan lokaci.
Bayan ya dawo aka shirya amma na ciki na ciki domin tsakaninsa da shugabannin majalisar sai da gaisuwa da yake hakoran karya.
Sabuwar majalisa
Dawowar sa ke da wuya sai kuma ya kakkabe hularsa ya koma yi wa wanda yayi wa adawa a wancan majalisa wato Femi Gbajabiamila aiki. Anan ne fa ya rika binshi a gindi a gindi domin ya tabbata cewa akalar a wannan karon ya karkata ne ga Gbajabiamila.
Babu irin cin mutuncin da bai yi masa ba a lokacin da yake yi wa Yakubu Dogara aiki a wancan majalisar.
Shiko Gbajabiamila ya amshe shi hannu bibbiyu, ya nada shi babban darektan kamfen din sa na neman shugaban majalisar.
Abdulmumini ya rika saka wa a shafunansa na sada zumunta a yanar gizo ya na nuna cewa lallai fa yana aiki domin tabbatar da gani Gbajabiamila ya yi nasara babu dare babu rani.
Sai dai kuma hakarsa bai cimma ruwa ba domin ko mataimakin kwamiti na majalisa bai samu ba. Duk da kadifiri da ya rika yi yana zakewa sai Gabjabiamila ya yi nasara bai haifar masa da da mai ido ba.
Babban dalili kuwa shine kowa yana yin hannunka mai sanda ne da shi. Domin irin haka yayi wa Dogara ya kuma nemi ya kwance masa zani a Kasuwa a wancan majalisar.
Yanzu dai kaf cikin jerin sunayen kwamiti 102 da aka yi wa shugabanni da mataimaka babu sunan Abdulmumini a ciki. Dama kuma can ana ta rade-radin wai za a yi masa minista. Anan ma shiru ya ji. Masu sharyi sun jingina hakan ga kaffa-kaffa da ake yi da shi kada kuma ya samu wani abin ya sake karade duniya yana tonon silili.