Nan da wata biyu masu zuwa Najeriya za ta rabu da cutar Shan-Inna – WHO

0

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa nan da watanni biyu masu zuwa Najeriya za ta zama kasar da ta rabu da cutar shan-inna.

WHO ta sanar da haka ne a wata takarda da shugaban yada labarai, Charity Warigon ta rabawa manema labarai a Abuja ranar Talata.

“Najeriya za ta zama kasar da ta rabu da shan inna ne idan ta cika shekaru uku cutar ba ta bullo ba a kasar sannan nan da watanni biyu kasar za ta samu wannan matsayi da take hangowa.

“ Kasar ta samu wannan nasara ne a dalilin zakewar da ta yi wajen wayar da kan mutane game da yi wa ‘ya’yan su allurar rigakafi da kuma maida hanklali da shugabanni suka yi.

“Ko da yake hare-haren Boko Haram, rashin kudi da rashin karfin garkuwar jikin yara na daga cikin matsalolin da suka so yi wa wannan aiki kafar angulu amma hakan basu ne suka hana kasar zage damtse wajen cimma burin ta ba.

Warigon ta ce gwamnatin kasar ta dauki wasu matakai da za su taimaka mata wajen ci gaba da samun nasarori irin haka a nan gaba.

Wadannan matakai kuwa sun hada da inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko dake kasar, hada hannu da kasashe makwabta domin ci gaba da wayar da kan mutanen game da cutar, inganta hanyoyin gano cutar da hada hannu da kungiyoyin bada tallafi domin samun kudaden da ake bukata.”

A makon da ya gabata ne gidauniyar Bill Gates da Dangote suka jadadda cewa za su ci gaba da tallafa wa Najeriya wajen yaki da kawar da cutar shan inna a ƙasar.

Share.

game da Author