Jam’iyyar APC ta bayyana cewa duk dan takarar gwamna a zaben fidda-gwanin jihar Kogi da Bayelsa, zai sayi fam ne a kan naira milyan 22.5.
Sannan kuma ta ranakun da za a fara sayar da fam da kuma zaben fidda gwanin ‘yan takara.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC dai ta bayyana ranar 16 Ga Nuwamba, 2019 ce za ta gudanar da zaben gwamna a Bayelsa da kuma Kogi.
Sakataren Tsare-tsaren APC na Kasa, Emma Ibediro ne ya bayyana ka’idojin da APC ta dauka, a jiya Talata a Abuja.
Ibediro ya kara da cewa tantebur din tsare-tsaren zaben fidda gwanin da APC za ta gudanar, yay i daidai da ka’idojin zabe wadanda Dokar Zabe ta 2010 ta shimfida. Haka kuma yayi daidai da sharuddan da INEC ta gindaya.
Ya ce za a fara sayar da fam ranar yau Laraba, 10 Ga Yuli, a kan kudi naira milyan 22.5. za a ci gaba da sayarwa a hedikwatar APC ta Kasa da ke Abuja, tun daga ranar har zuwa ranar 20 Ga Agusta, ranar da za a rufe sayar da fam din.
Sannan kuma duk wanda ya sayi fam, to ya tabbatar da cewa ya maida wa hedikwatar APC fam din na sa da ya cike, daga ranar da ya saya zuwa ranar 21 Ga Agusta, ranar da za a rufe karba.
“Ranar Alhamis, 22 Ga Agusta, 2019 ne za a tantance ‘yan takara, sannan kuma ranar Juma’a, 23 Ga Agusta za a bi ba’asin duk wani korafe-korafe da ka iya biyo baya.”
Daga nan kuma y ace za a gudanar da zaben fidda-gwani a ranar 29 Ga Agusta.
Discussion about this post