Wani kwakkwaran bincike ya tabbatar da cewa Shirin Bayar da Rance ga manoman karkara ya inganta kuma ya kara yawan dubban jama’ar karkara masu mu’amala da bankuna. Haka dai wata kungiyar bincike mai suna EFInA ta bayyana.
PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa dubban wadanda suka ci gajiyar shrin bayar da lamuni ga manoman karkaka (Anchor Borrowers’ Programme’ a Arewa a Jihohin Sokoto da Kebbi.
Kamar yadda binciken ya nuna ta hanyar tattaunawa da jami’an aiwatar da shirin da wasu jama’ar karkara mazauna kananan hukumomin da ke cikin lungu, an gano cewa shirin wanda gwamnatin tarayya ta fito da shi, zai kara shigar da jama’ar da aka yi wa nisa sosai a cikin harkokin inganta sana’ar noma tare da tsarin tasarifi.
Sai dai kuma bincike ya kara nuna cewa fadada shirin shigar da mazauna karkara karbar harkar bankin gadan-gadan fiye da masu cin moriya shirin na rage wa talakawa radadin kuncin rayuwa kadai.
Shirin Bayar da Rance Ga Manoma, ABP shiri ne da gwamnatin Muhammadu Buhari ta shigo da shi musamman domin tallafa wa manoma samun damar noma amfanin gonar da za su rika sayarwa.
Tashin farko a lokacin da aka kirkiro shirin, Babban bankin Tarayya (CBN) ya ware naira bilyan 40 daga cikin Gidauniyar Inganta Kanana da Matsakaitan Manoma wadda ke da zunzurutun kudade har naira bilyan 220.
An rika bayar da rance a kan kudin ruwa kashi 9 bisa 100 kacal na adadin kudaden da manomi ya ranta.
Ta dalilin karbar wadannan kudade, an samu ambaliyar wadanda suka rika bude asusun ajiya a banki, domin mallakar lambar BNV, wacce da ita ce ake tura wa manomi kudaden da aka ramta masa.
“Dalilin wannan ramce da dama daga cikin mu mun bude asusun ajiya a banki tare da mallakar lambar BVN. Domin wannan tilas ne ga mai son ya karbi ramce kudaden.”
Haka wani malamin addini Musulunci mai suna Malam Kashibu, wanda ya koma harkar noma gadan-gadan ya furta, ta hannun wani mai yi masa tafinta.
Kafin kaddamar da shirn ABP, akasarin manoman Sokoto da na Kebbi duk ba su yin ajiya ko wata harka da banki.
Mutane da yawa sun tabbatar PREMIUM TIMES haka, ciki kuwa har da tsohon Kwamishinan Ayyukan Gona na Kebbi, Garba Dadinga da kuma Shugaban Kungiyar Manona Shinkafa na Jihar Sokoto, Salihi Ibrahim.
KALUBALEN DA MANOMAN AREWA KE FUSKANTA
Manoman karkara a Arewa maso yamma sun kasance koma-baya wajen yin amfani da banki. Kashi 62 bisa 100 na manomanyankin ba su amfani da banki.
Sai dai kuma shi Alhassan Jega cewa ya yi abin ya dogara ne da yawan marasa ilmin zamani, wadanda kuma su ne suka fi suka fi yawa sosai idan ana batun noma.
Haka abin ya ke a karamar hukumar Goronyo ta jihar Sokoto da sauran wurare,
Akwai kuma matsalar talauci, wanda kowa ya na ta kan sa da kuma ta cikin sa. Wannan ya na hana talaka yin tattalin da zai samu damar kai ajiya banki.
Nisa da karancin bankuna na daga cikin dalilian da wasu manoma suka bayar a Goronyo a kan dalilin da ya sa ba su ajiya a bankuna.
Dukkan wadannan dalilai sun taru sun sun hade da babar matsalar rashin ilmin zamani.
Sai dai kuma idan aka kwatanta da 2017, za a iya cewa an samu ci gaba sosai.