RAHOTON MUSAMMAN: Yadda Tsarin Tradermoni da Rage Radadin Talauci Suka Kasa Inganta Rayuwar Talaka

0

Shu’aibu Sani da ke kauyen Gidan Tsika a cikin Karamar Hukumar Kiyawa ta Jihar Jigawa, ya na daga cikin wadanda suka ci moriyar kudaden tallafin CCT.

Shirin CCT, wato ‘Conditional Cash Transfer, shiri ne na bai wa talakawa tallafin kudi naira 5,000 duk wata, domin rage radadin talauci.

Shu’aibu ya ce wata biyu ake hadawa sannan a bashi naira 10,000, amma duk da haka ya na kokari ya na yin tattalin tara naira 600 daga cikin kudaden.

Hausawa na cewa ‘kowa ya ci zomo, to ya ci gudu.’ Wannan magana ta yi daidai idan aka kwatanta da irin jidalin da Sani ke tsintar kan sa a ranar da ya je karbo wadanne kudade.

Sani kan bar kauyen su tun da sassafe da nufin ya kasance ya riga kowa isa wurin karbar kudin da ke da tazarar kilomita biyu daga kauyen na su.

Ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa a duk ranar da zai je karbar kudin, to zai yini bai yi aikin komai a gida ba, duk kuwa dasubancin da yay i wurin zuwa karbar kudin, wanda lalowa za a yi a kirga, a damka maka.

Wani mai suna Isyaku Ibrahim wanda shi ma dan kauyen su Sani ya fito, y ace baii taba yin tattalin adana ko kwandala ba daga kudin ya ke karba.

Sai ma korafi da yay i ga wakilin Premium Times cewa yak an bar harkar noma da kasuwancin da ya key i, domin maida hankalin sag a karbo wannan naira 5,000 kacokan. Ya kara da cewa sannan kuma ana bukatar ka bai wa dagacin kauyen ku wani dan hasafi daga cikin kudin.

An kafa wannan tsarin bayar da kudi a cikin 2016 a matsayin wani shiri daga cikin tsare-tsaren gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na rage radadin talauci da inganta rayuwar talakawa.

Cikin Afrilu, Shugabar Shirin Maryam Uwais ta shaida cewa sama da mutane 300,000 ne suka amfana da shirin tallafin.

Shi kuma jami’in tsare-tsaren shirin na kasa, Temitope Sinkaiye, y ace daga lokacin da aka fara zuwa yanzu, an raba naira bilyan 1.5 a cikin jihohi 26.

Kudin Tradermoni

Wannan shiri ya sha suka sosai a fadinn kasar nan. Shi ma shiri ne kamar CCT, wanda ake bai wa jama’a kudade kai-tsaye. Sai dais hi wannan shiri ramcenn kudi ne za a ba ka da niyyar za ta biya.

Idan ka biya ka na neman a kara maka, to za a iya kara maka nunkin wanda aka ba ka daga farko. Shi kuwa shirn CCT kyauta ce gwamnati ke raba kudaden a matsayin tallafin rage radadin talauci.

An rika cewa shirin Tradermoni sayen kuri’u ne, musamman ganin yadda Maimakin Shugaban Kasa ya jajirce a lokacinn kamfen ya na tallata shirin. Sannan kuma bayan kammala zabe, babu wanda ya kara jin Yemi Osinbajo ya na maganar tradermoni.

A farkon fara shirin dai gwamnati ta ce ta kudiri aniyar bai wa mutane milyan biyu lamunin wanda ke faraway daga naira 10,000. Amma fa har yanzu babu takamaimen adadin da suka amfana da hirin.

Kusan duk wani dan Jigawa da ya karbi lamunin, to babu wanda ya biya har yanzu. Wani mai saida kayan miya da ake kira Sa[idu Ali da ke Kasuwar ‘Yan Tipper, Dutse, cewa ya yi shi da ya ga ana bada kudaden ba tare da an sha wahaka sosai ba, sai ya yi tunanin kamar kayauta ake bayar da kudin.

“Amma fa ni ina da niyyar biya.Sai dai ban san hanyar da zan bi na biya kudaden ba.”

Sai dai kuma masana harkokin tattalin kudade sun soki lamirin yadda a Najariya wannan Shin Rage Radadin Talauci bai yi tasiri ba kamar yadda yay i a Mexico da Indiya.

Da dama sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa rashin gudanar da tsarin ta hanyar bin ka’idojin matakai na jawo hankulan jama’a su rika amfani da bannkuna, ya na daga cikin dalilin da

Da dama daga masana harkokin kudade sun yaba wa shirin, amma kuma sun nuna dalilan da ya sa CCT da Tradermoni kin yin tasiri.

Sannan sun ce Shirin Baiwa Manoma ramce na ‘Anchor Barrowers ya yi tasiri sosai.

“Amma shirin bada kudaden kai-tsatye ya haifar da rashin sanin takamaimen yadda aka bayar da kudaden, mutnae nawa ake bai wa kuma bai kara yawan jama’r da ke amfani da banki na.

PREMIUM TIMES ta nemi jin ta bakin Maryam Usai, amma ba ta dauki kiran da aka yi mat aba, sannan kuma ba ta maida amsar sakon tes da aka yi mata ba.

Share.

game da Author