BUGU BIYU: Tabbatattun bayanai da ke a hannun PREMIUM TIMES sun tabbatar da yadda tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari ya bayar da kwangila daya sau biyu kuma ga mutum daya. Sannan kuma farashin kwangilar ya wuce-gona-da-iri.
Da farko an bayar da kwangilar gina rijiyoyin burtsatse 84 a fadin kananan hukumomi 14 na jihar a ga wani kamfanin kasar China mai suna China Zhonghao Nigeria Limited, a kan kudi naira bilyan 27.5. An bayar da kwangilar a cikin 2014.
Sai kuma aka dawo a cikin 2018 aka sake bayar da wannan kwangila kuma a kan wadancan adadin kudade, naira biliyan 27.5.
ZUKI-TA-MALLE: Babban abin tayar da hankali shi ne ita gwamnatin jihar a lokacin Yari, ta yi wa kwangilar kudi ne a kan gejin naira biliyan 19.7. Amma a ranar 3 Ga Oktoba, 2013, sai aka rubuta wa Manajan Darakta na kamfanin takardar amincewa da kwangilar a kan kudi naira bilyan 27.5. Wato an yi azuraren karin kusan naira biliyan 8 kenan, a bugun farko na kwangilar.
WALA-WALA: Yayin da aka zo wajen biyan kudi ga kamfanin, sai aka biya shi naira bilyan 19.3, maimakon naira bilyan 27.5 a cikin 2014.
Wannan bankaura ta faru ne a karkashin Ma’aikatar Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautun Gargajiya. Sannan kuma tuni kwamitin da sabon gwamna Bello Matawalle ya kafa a karkashin tsohon mataimakin gwamna, Ibrahim Wakkala ya tabbatar da haka.
Wato dai Yari ya kara wa wannan kwangila zunzurutun kudi har naira bilyan 8.2 kenan.
RUWAN BURTSATSE KO RUWAN BAGAJA?: Idan aka kwatanta da yadda aka bayar da kwangilar, kenan an gina kowace rijiyar burtsatse daya tal a kan kudi naira milyan 327.2
Ya zuwa 2019 dai an ce aikin gina rijiyoyin sun kusa kammaluwa da kashi 75 bisa 100.
Abin mamaki kuma shi ne sai aka dawo a cikin 2018 aka sake bayar da wannan kwangila akan wancan adadin kudade, kuma ga wancan kamfani na Chana.
Sai dai kuma gwamnatin jihar Zamfara ta cire naira biliyan 14.2 ta bayar kudin somi-tabin fara aiki. Wato kenan ana bin bashin cikon naira bilyan 13.3 kenan.
Takardun bayanan mika mulki da aka damka wa kwamiti daga Ma’aikatar Kananan Hukumomi Da Masarautu, sun tabbatar da cewa wannan kamfani ya na bin gwamnati bashin cikon naira bilyan 21.5, duk a kan kwangilar burtsatse.
Sai dai kuma ba a sani ba ko an bai wa kamfanin sabuwar kwangilar ce domin ya sake gina wasu rijiyoyin 84 a wasu wuraren ba.
Daya daga cikin mambobin wannan kwamiti mai suna Nura Almajiri, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa babu wata rijiya ko guda daya da aka gina ko’ina.
“ Mun karade ko’ina, amma ko gurbi daya na rijiya ba mu gani ba, balle kuma burtsatse.”
BAN CI NANIN BA – Yari
Yayin da kakakin tsohon gwamna Yari, wato Ibrahim Dosara ya karyata cewa an yi wannan tabargazar, ya kara shaida wa PREMIUM TIMES cewa ya kamata ta je Jihar Zamfara da kan ta domin ta ga shin an yi aiki ko kuwa ba a yi ba.
Shi ma daya daga cikin jami’an kamfanin ya ki cewa komai yayin da PREMIUM TIMES ta tuntube shi.
ASARKALA DA SABARKALA: Tsakanin 2014 da 2018 gwamnatin Yari ta karya dokokin bayar da kwangila da ke cikin kundin tsarin mulkin Najeriya ta hanyar bai wa kamfanin da ba shi da rajista kwangila ta bilyoyin nairori.
Domin daka ta ce sai kamfanin da ke da rajista da Hukumar Yi Wa Kamfanoni Rajista ta Kasa (CAC) ne kadai ya wajaba a bai wa kwangila. Shi din ma, sai wanda ya cika wasu tsauraran sharuddan da gwamnati ta gindaya.
PREMIUM TIMES ta ga wasu bayanan yadda gwamnatin Abdulaziz Yari ta bayar da wasu kwangiloli 44 ka kamfanoni 44, wadanda dukkan kwangilolin akasari na ginawa ne da kuma gyaran msallatai da makarantun Islamiyya a fadin kananan hukumomin jihar 14.
An yi wadannan ayyuka akan naira miliyan 543, amma an biya naira miliyan 401, saura cikon naira milyan 142 kenan.
Daga cikin wadannan kwangiloli 44, guda 7 ne kadai aka bai wa kamfanoni 7 masu rajista. Wasu ma daidaikun mutane kawai aka dauka aka bai wa ba tare da su na da kamfani ko na tuyar kosai ba.
An nuna cewa an kammala wasu ayyukan, amma wasu kuma an ce ana kan aikin su.
Sai dai kuma Dosara ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa gwamnatin Yari ba ta taba bai wa kamfanin da ba shi da rajista kwangila ba. Daga nan sai ya ce a iya zuwa hedikwatar CAC a bincika, domin a tabbatar.
Idan ba a manta ba, a jiya Talata ne PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda Kwamitin Karbar Mulki da Bincike wanda Gwamna Bello Matawallev na jihar Zamfara ya kafa, ya yi zargin cewa tsohon gwamnan jihar, Abdul’aziz Yari ya yi wa naira bilyan 2501.9 hadiyar-kafino.
Hakan ya fito fili ne jiya Litinin a lokacin da Shugaban Kwamitin, kuma tsohon Mataimakin Gwamna na Yari, Ibrahim Wakkala.
Wakkala ya ce: “Kwamiti na a lokacin da tantance yawan basussuka da tabargazar da gwamnatin da ta sauka kwanan nan ta tafka a karashin Abdul’aziz Yari, ta bi ta karbi rahoton da shi Yari din kafa masu binciken sa suka gudanar kafin saukar sa.
“ Mun bi wannan hanya, mun dawo mun sake bin wata mu na nema, amma mun rasa inda zunzurutun kudade har naira bilyan 250 suka shige.
“ Daga cikin wadannan kudade kuwa har da tulin bashin naira biliyan 115,190,477,572.00 wadanda ba a kai ga biyan masu ayyukan kwangilolin da aka rubuta ana gudanarwa ba har 462.
“Akwai kuma kudin garatutin ma’aikata har naira biliyan 1,431,645,305.99
“Sannan kuma Hukumomin Shirya Jarabawa na bin Jihar Zamfara basussukan NECO da na WAEC har naira biliyan 2.8” Inji Wakkala.
Ya kara da cewa gwamnatin Yari ta fitar da naira biliyan 2 da nufin biyan garatutin ma’aikata, amma an gano cewa naira milyan 400 kadai ta biya ga Manyan Sakatarorin da suka yi ritaya kawai.
An rasa yadda aka yi sa sauran cikon naira biliyan 1.6, kamar yadda rahoton Wakkala ya wallafa.
Sai dai kuma Kakakin Yada Labarai na Yari, Ibrahim Dosara, ya ce duk babu gaskiya a cikin bayanan kwamitin.
“Karairayi ne kawai, amma ka jira na dawo daga Umra zan ba ka cikakken bayanin komai dalla-dalla.”
Haka Dosara ya shaida wa wakilin PREMIUM TIMES ta wayar tarho.