Cikin Kwana 90 Talauci Zai Ragu Idan Aka Bawa Kananan Hukumomi Kudinsu, Daga Mustapha Soron Dinki

0

A tsarin Federaliya, gwamnati ta kasu gida uku : Gwamnatin tarayya, jiha da kuma karamar hukuma.

Karamar hukuma itace karama a cikinsu, kuma tana da ikon gudanarwa kamar yadda doka ta bayar, duk da akwai ‘dan rudani akan hakan saboda doka ta bata ‘yanci kuma ta bayyanata a matsayin wani yanki na jiha.

Bayyana karamar hukuma a matsayin ‘Agent of state’ ya bawa jihohi damar wuce gona da iri wajen lankwame kananan hukumomin.

Talaucin karamar hukuma ne ya shafi talaka, tunda mulkin karamar hukuma yafi kusanci dashi.

Babban dalilin da yasa aka samar da karamar hukuma shine, saboda a kawo gwamnati kusa da talaka.

Ko yin hakan ya biya bukata a Najeriya?

Gaskiyar lamari, duk da zargin cin hanci da rashawa, kananan hukumomi sun yi tasiri matika a baya wajen warware kananan matsalolin al’umma a lungu, saqo da kauyuka.

Mai karatu, Comrade Soron Dinki dan Kano ne, don haka zan takaita misalaina akan Kano saboda nan nafi sani.

Babu shakka a lokacin da karamar hukuma take da cikakken ‘grant’ a Kano, duk da cin hanci da ake zarginta dashi, talakawa suna jin tasirinta a rayuwarsu.

Kuma dama duk gwamnatin gaske tana samar da tarinta ne a cikin rayuwar al’umma.

Akwai mutane da yawa da suke neman abinci a iya karamar hukuma.

Misali, akwai ‘yan kwangila da wadanda suke aiki a karkashinsu da yawa, akwai ‘yan kasuwa, akwai dalibai, akwai kuma manoma da masu sana’o’in hannu.

A wancen lokacin, ciyaman da kansilolinsa suna da tasirin gaske wajen samar da cigaba da sanin matsalolin talakawa duba da yadda wasu daga cikinsu suke gudanar da ayyuka tare da talakawan ma.

Amma yanzu gwamnati ta zama kashi biyu : Gwamnatin tarayya da gwamnatin jiha.

Gwamnoni sun mayar da karamar hukuma kango, shugabancinta ya zama tsilla-tsilla saboda babu abun yi, an kashe siyasar ta, gwamnoni sun kwace mata “financial autonomy”.

Marx Weber yace, babu iko ko shugabanci (Power or Authority) idan mutum bashi da damar gudanarwa ko tursasawa a gudanar.

Hausawa suka ce, da baqi-qirin gwara baki-baki. Duk lalacewar karamar hukuma tafi rashinta amfani. Idan ance ana sata a cikinta, yanzu satar raguwa tayi?

Gwara waccen satar ma tunda talaka yana amfanarta, abu ne shahararre a Najeriya a samu gwamna shi kadai ya saci biliyan 25.

Gaskiya naji dadi da naji Buhari zai dawo da hayyacin kananan hukumomi.

Tabbas, bayan yin hakan, yakamata a kar6e zabensu daga hannun gwamnoni saboda suna kunyata siyasar Najeriya don ba za6e suke yi ba, wasan yara ne.

Akwai bukatar a rushe hukumomin zaben jiha saboda gwara zaben da daliban jami’o’i suke yi a cikin makaranta da zaben kananan hukumomin da SIECs suke yi a jihohi.

Kuma zan so Buhari ya kirkiro musu hukuma mai zaman kanta bayan ‘local government service commission da ministry for local government’ wadanda suke ‘yan amshin shata ga gwamna, yin hakan zai basu tasiri sosai a jihohin da suke kuma zai rage musu cin hanci da rashawa.

Allah ya shiryar damu.

Share.

game da Author