Kamar yadda aka sani cutar kwalara ko kuma cutar amai da zawo cuta ce dake yawan sa mutum yin bahaya da amai sannan rashin gaggauta daukan mataki kan iya yin ajalin mutum a cikin lokaci kalilan.
Kwalara a kasashe kamar Najeriya tsohuwar cuta ce da har yanzu cutar ta ki ci ta ki cinyewa. Sannan bayanai sun nuna cewa cutar ta fi addabar mutane a lokacin damina.
Sakamakon binciken kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ya nuna cewa mutane miliyan 2.9 na kamuwa da cutar inda daga ciki mutane 95,000 ke rasa rayukan su duk shekara a kasashen da suke samun ci gaba.
Bisa ga bayanan likitocin hanyar kamuwa da wannan cutar shine rashin tsaftace wurin zama wato muhalli. Hakan na nuna cewa rashin tsaftace muhalli, rashin amfani da ruwa mai tsafta, rashin wanke hannu bayan an yi amfani da ban daki, rashin wanke hannu kafin da bayan an ci abinci duk sune sanadiyyar kamuwa da cutar.
Sauran hanyoyin kamuwa da cutar sun hada da rashin cin abincin dake inganta garkuwan jikida sannan mai dauke da cutar kanjamau.
Domin samun mafita daga cutar hukumar hana yaduwar cututtuka na kasa (NCDC) ta bayyana cewa ta gano wasu kananan hukumomi 83 da suka fi yawan fama da bullowar cutar akai-akai.
NCDC tabbatar da haka ne a sakamakon wani bincike da ta gudanar kan yawan bullowar cutar tsakanin shekaru biyar da suka gabata wato daga 2012 zuwa 2017.
Sakamakon binciken ya nuna cewa jihohin Zamfara, Bauchi da Kano na daga cikin jihohin da suka fi fama da wannan cuta a Najeriya.
NCDC ta ce zata maida hankali matuka wajen ganin cutar bai yadu ba a wannan shekara ta hanyar yin tanadin isassun alluran rigakafi, yi wa mutane rigakafin cutar sannan da wayar wa mutane kai game da hanyoyin guje wa kamuwa da cutan.
Alamun kamuwa da cutar kwalara.
1. Zazzabi.
2. Amai da gudawa.
3. Rashin jin karfi a jiki.
4. Rashin iya cin abinci
5. Suma.
Hanyoyin gujewa kamuwa da cutar.
1. Tsaftace muhalli.
2. Wanke hannu da zaran an yi amfani da ban daki.
3. A guji yin bahaya a waje.
4. Amfani da tsaftattacen ruwa.
5. Wanke hannu kafin da bayan an ci abinci.
6. Cin abincin dake inganta garkuwan jiki.
7. Yin allurar rigakafi
8. Zuwa asibiti da zaran an kamu da cutar.