Godiya tatabbata ga Allah mai Girma da daukaka, Mai kamala a cikin sunayensa, Allah ya kara tsira da aminci ga shugabanmu Annabi Muhammadu da iyalansa da sahabbansa baki daya.
Babu shakka an umurci musulmi da ya lizimci Ibada da tsare dokokin Allah. Hakan zai tsarkake zuciyar sa. Allah ya shar’anta Ibadu kala-kala, na wajibi da na farilla kamar azumi.
Azumin sittu shawwal wata zinariyar garabasa ne da Allah ya azurta wannan al’uma da shi. Annabi Muhammadu (SAW) ya kwadaitar da yin azumin kwanaki shida a cikin watan Shawwal bayan an yi azumin watan Ramadan. An karbo daga Abu Ayuba (R.A) cewa Annabi Muhammadu (SAW) yace: wanda ya azumci ramadana kuma ya bi bayan sa da azumin kwanaki shida daga shawwal, to kamar, ya yi azumin shekara ne.
Azumin watan Ramadana yana dai dai da azumin watanni goma, azumin kwanaki shida na Shawwal suna dai dai da watanni biyu. Domin ana ninka kyakkyawan aiki
niki gama ko fiye da goma.
Yin azumin kwana shida bayan Ramadan, a cikin shawwal, yana nuna godiyar bawa ga ubangijin sa, ga falalar da ya yi masa na yin azumin ramadana, kuma kokarin yawaita ayyukan alhairi ne da biyayya ga Allah a cikin bauta. Yana daga cikin falalar azumin Shawwal, cike gibin da
nakasun da bawa ya samu a cikin azuminsa na Ramadana. Kuma alama ce da ke nuna karbuwan azuminsa na ramadana.
Abinda akafi so shi ne ayi azumin a jere, amma idan anyi su da ban-ban babu laifi.
Allah muke roko ya tsremana Imaninmu da mutuncinmu kuma ya karbi Ibadunmu. Amin.