Kotu ta umarci INEC ta mika wa Okorocha Satifiket

0

Babban kotu dake Abuja ta umarci hukumar zabe da ta gaggauta mika wa tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha kuma wanda ya lashe zaben sanata a jihar Satifiket din lashe zabe.

Idan ba a manta ba hukumar zabe ta ce ba zata mika wa Okorocha Satifiket ba saboda jami’in zabe da ya bayyana sakamakon sa a wancan lokacin ya bayyana cewa da karfin tsiya aka tilastashi ya bayyana cewa Okorocha ne ya lashe zaben.

Bayan haka kuma kotu a jihar Imo ta umarci hukumar da ta dakatar da ba shi Satifiket din tukunna bisa wannan zargi.

Sai dai kuma ba a nan ne gizo ke sakar ba domin duk da wannan hukunci na kotu, wata kotu a Abuja kuma ta umarci hukumar da ta yi maza-maza ta mika masa Satifiket din cewa hukumar ko wani bashi da ikon sakawa ko ya hana sai dai shi jami’in zaben da ya gudanar da zaben sannan kuma ya bayyana sakamkon zaben.

Kuma a bisa dukkan takardun dake gabanta, malamin zaben da ya kula da zaben a wannan shiyya shine ya bayyana cewa Okorocha ne ya lashe zaben.

Hukumar zabe ta ce tana nan tana duba hukuncin wannan kotu duk da cewa akwai wani a gabanta kuma nan ba da dadewa ba zata bayyana matsayinta.

Share.

game da Author