Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari, ta kalubalanci jami’an tsaro da su gaggauta kawo karshen mahara da ke karkashe jama’a bagatatan, da sauran matsalolin tsaro a kasar nan.
Aisha ta yi wannan kakkausan kira a Katsina yayin da ta ke raba kayar agaji da tallafi wurin ‘yan gudun hijira sama da 25,000, wadanda mahara ko ‘yan bindiga suka fatattaka daga kauyukan su.
Aisha ta ce ya zama dole a kakkabe wadannan ‘yan bindiga, kafin su kai ga kakkabe al’umma gaba daya.
“Ko dai jami’an tsaron mu su taimaka a kawo karshen wannan fitina, ko kuma su zauna su bari ‘yan bindiga su kakkashe jama’a baki daya.” Inji ta.
Ta ci gaba da cewa ya kamata manya da dukkan sauran masu mutunci da kishin kasa su rika fitowa su na magana idan sun ga ana aikata ba daidai ba. ta ce wannan zai kara sa a dauki matakin gaggawa.
“Bai kamata a ce mun zo nan mu na raba shinkafa, madara da sauran kayan masarufi ga wadanda mahara suka fatattaka a lokacin watan Ramadan ba.
“Mu dai na yin shiru a lokacin da abubuwan takaici ke faruwa, mu na tsamman wai idan abu ya faru yau, to ba zai faru gobe ba.
“Ina kara fada muku cewa abin da ya faru yau, to gobe ma sake faruwa zai yi. Jibi ma idan kowa ya yi shiru, zai sake faruwa.
“Ya zama dole kowa ya tashi ya fito ya na fadar gaskiya. Saboda bai kamata ba mu bada kuri’u mafiya yawa a lokacin zabe, sannan kuma mu bar mahara na ci gaba da kashe jama’a kuma a yi shiru.
“Dole mu rika yin magana a duk abin da ke tadfiya ba daidai ba.” Inji Aisha.
Aisha ta ce kayan agajin da suka kai ba na gwamnatin tarayya ba ne, gudummawa ce ita da matan tsoffin gwamnonin Nasarawa, Bayelsa, Adamawa, Akwa Ibom suka hada kudi ska sayo kayan abincin.
Tun da farko Hakimin Katsina, Aminu Abdulmumini, ya gode wa uwargidan ta Shugaba Muhammadu Buhari.
Ya yi kira ga gwamnati da ta kara kaimi wajen magance mahara masu kashe jama’a.
“Wadannan mutane su na bukatar gudummawa, amma fa sun fi bukatar ganin cewa gwamnati ta shawo kan wannan fitina.
“A kowace rana sai mun rika jin karar jiragen yaki su na shawagi, amma kuma ‘yan bindiga ba su daina kashe mutane ba. Ba mu san abin da ke faruwa ba.” inji Hakimin Katsina.
Wadannan masu gudun hijira sun fito ne daga kananan hukumomin Batsari, Kurfi, Faskari, Danmusa, Safana da Kankara.