Sanata Dino Melaye ya tabbatar da cewa zai fito takarar zaben Gwamna Jihar Kogi.
Melaye ya fadi haka ne inda ya tabbatar da gaskiyar ji-ta-ji-tar da aka fara yadawa cewa zai fito ya nemi takarar gwamnan Kogi.
Melaye, wanda shi ne Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma, ya samu nasarar sanata a karo na biyu a karkashin PDP, kuma a PDP din ne zai shiga takarar gwamnan.
Jaridar PUNCH ta ruwaito sanatan ya yi wannan furuci a karon farko a fili, a lokacin da ya halarci wani taro a gidan Manjo Janar David Jemebewon mai ritaya.
Taron dai ya samu halartar shugabannin jam’iyyar PDP, kamar yadda jaridar ta ruwaito.
A wata gajerar amsa da Melaye ya bai wa PREMIUM TIMES jiya Asabar bayan ta tuntube shi domin ta ji ta bakin sa, sanatan ya ce “tabbas gaskiya ne” zai yi takar gwamnan Kogi.
Amma dai bai kara yi wani bayani ko karin haske a kan batun takarar ta sa da ya ce ya dauri aniyar yi ba.
Idan har PDP ta tsaida Dino Melaye, to zai yi gwagwagwa ne da babban abokin hamayyar siyasar sa, Gwamna Yahaya Bello na APC.
Za a gudanar da zaben gwamnan jihar Kogi a ranar 6 Ga Nuwamba.
Discussion about this post