Gwamnatin Yobe ta hana zirga-zirgar ababen hawa a lokuttan sallar Idi

0

Gwamnatin jihar Yobe ta sanar da hana zirga-zirgar ababen hawa tun daga karfe 10 na daren Litini zuwa 10:30 na safiyar Talata.

A sanarwar da darektan yada labaran gwamnatin jihar yayi, Abdullahi Bego ya ce gwamnati ta yi haka ne domin a samar da tsaro a lokuttan da ake sallar Idi a fadin jihar.

” Gwamna Mala Buni yana yi wa mutanen jihar Yobe fatan Alkhairi da fatan ayi sallah lafiya.”

Share.

game da Author